Biki Wan Shagali: APC Ta Shirya Gagarumar Tarba ga Gwamna Mutfwang

Biki Wan Shagali: APC Ta Shirya Gagarumar Tarba ga Gwamna Mutfwang

  • Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya
  • Jam'iyyar APC reshen jihar Plateau ta shirya gagarumin biki domin tarbar gwamnan zuwa cikinta a shekarar 2026
  • Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya nuna cewa sauya shekar Gwamna Mutfwang za ta kara karfafa jam'iyyar

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Jam’iyyar APC ta sanar da shirin tarbar gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, wanda ya sauya sheka daga PDP.

Jam'iyyar APC ta shirya gagarumar tarba a watan Janairu domin maraba da gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang.

Jam'iyyar APC za ta tarbi Gwamna Caleb Mutfwang
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang da tambarin jam'iyyar APC Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce an bayyana hakan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Disamban 2025 ta bakin sakataren yaɗa labarai na APC a Plateau, Shittu Bamaiyi, bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jos.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi sabon shugaba bayan gudanar da babban taronta na kasa

Jiga-jigan jam'iyyar APC sun hadu a Plateau

Taron ya samu halartar manyan shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da tsohon gwamnan jihar, Simon Lalong, jaridar Leadership ta dauko labarin.

An bayyana taron a matsayin wata muhimmiyar dama ta tarbar gwamnan tare da karfafa gwiwar mambobin jam’iyya a fadin jihar.

Ko da yake sanarwar ba ta bayyana takamaiman ranar liyafar ba, ta jaddada cewa taron zai kasance mai armashi da kima, tare da nuna cewa sauya shekar Mutfwang na nuni da babban sauyi a yanayin siyasa a jihar Plateau.

"Jam’iyyar APC na shirin tarbar Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau a watan gobe. Wannan liyafa za ta nuna cewa, da shigowarsa jam’iyyar, duk jihar Plateau ta koma APC.”

- Shitu Bamaiyi

Nentawe ya yaba da sauya shekar Mutfwang

A yayin taron, Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa sauya shekar Mutfwang zai karfafa tare da haɗa kan APC a jihar Plateau, tare da tabbatar da tsari guda a jam’iyyar gabanin zaɓubbuka masu zuwa.

Kara karanta wannan

Musulmai sun yi rashi: Shugaban kotun shari'ar Musulunci ya riga mu gidan gaskiya

Ya kuma yi kira ga dukkan mambobi da su shiga rajistar yanar gizo ta jam’iyyar domin a tabbatar da su a matsayin ingantattun mambobin APC.

Za a ba mambobin jam'iyyar APC kyauta

A gefe guda kuma, Yilwatda ya sanar da kyautar Kirsimeti ta manyan motoci 11 na shinkafa, da za a raba wa mambobin jam’iyyar a fadin jihar Plateau, a matsayin godiya ga goyon bayan da suke bayarwa.

Taron masu ruwa da tsakin ya samu halartar fitattun mutane da dama, ciki har da Sanata Diket Plang, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ahmed Wase, Dr. Babayo Gagdi, John Dafa’an, Dalyop Fom, da kakakin majalisar dokokin jihar Plateau, Naanlong Daniel.

Sauran sun haɗa da Sanata I.D. Gyang, Victor Lar, Hezekiah Dimka, tsohon sakataren gwamnatin jihar (SSG) SD Lot, John Gobak, Dr. Cyril Tsenyil, Dr. Umar Mantu, Farfesa Artu, da Janar John Sura (mai ritaya), tare da sauran manyan shugabanni.

APC ta shirya gudanar da babban taro

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shirya gudanar da babban taronta na kasa.

Kara karanta wannan

Ziyarar Tinubu: Gwamnatin Bauchi ta aika sako ga mutanen jihar

Jam'iyyar APC ta shirya gudanar da babban taron ne a cikin shekarar 2026 domin zabar shugabannin da za su jagorance ta.

Kafin babban taron, za a fara da zaben shugabannin jam'iyyar a matakin gundumomi, kananan hukumomi da jihohi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng