Babbar Magana: An Fara Neman a Tsige Bola Tinubu daga Kujerar Shugaban Kasa
- Jam'iyyar PRP ta nuna damuwa kan zargin da ake na sauya wasu sassan dokokin haraji bayan majalisar tarayya ta amince da su
- Tuni dai Majalisa ta kafa kwamitin wucin gadi da zai gudanar da bincike kan banbanci tsakanin dokokin da ta amince da su da wadanda ke hannun gwamnati
- PRP ta bayyana cewa matukar aka samu Shugaba Bola Ahmed Tinubu da hannu a wannan aikin, tana kira da a tsiga shi nan take
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dambarwar canza dokokin sake fasalin haraji a Najeriya na ci gaba da daukar hankali yayin da jam'iyyun siyasa suka fara bayyana matsayarsu.
Jam’iyyar PRP ta yi kira da a tsige Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga mukaminsa idan aka tabbatar da cewa yana da hannu a murɗawa ko sauya dokokin haraji da Majalisa ta amince da su.

Source: Twitter
Jam’iyyar ta yi Allah-wadai da abin da ta kira sakaci da ƙa’idojin mulki da kuma nuna halin ko-in-kula kan kundin tsarin mulki da gwamnatin tarayya ke yi, in ji rahoton Leadership.
Majalisa ta fara daukar mataki
Idan baku manta ba Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin bincike na mutum bakwai domin bincikar zargin da ake yi na sauya dokokin haraji da ta amince da u.
Ana sa ran kwamitin zai gudanar da bincike mai zurfi don gano bambancin da ke tsakanin dokokin haraji da Majalisa ta amince da su da kuma idokokin da aka wallafa a jaridar gwamnati.
Da take mayar da martani, jam’iyyar PRP ta ce idan aka samu hujjojin da ke nuna cewa Shugaba Tinubu yana da hannu a wannan zargi, to ya dace a tsige shi nan take.
A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Falalu Bello, ya fitar, PRP ta bayyana cewa babu wanda ya fi iarfin doka, har shi kansa shugaban kasa.
PRP ta fadi sharadin tsige Tinubu
Ta ce lamarin na nuna cewa bangaren zartarwa na gwamnati ya riƙa sauya dokoki a ɓoye bayan Majalisa ta amince da su, ba tare da sahalewar ‘yan majalisa ba, in ji Daily Trust.
“Wannan aiki na rashin gaskiya daga bangaren zartarwa, wanda ya haɗa da ƙara wasu sassa, cire wasu, ko sauya muhimman tanade-tanade bayan doka ta riga ta samu amincewar Majalisa, na nuna raini ga tsarin mulki.
"Idan aka samu hujjojin da ke nuna Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da hannu a wannan laifi, PRP na kira da a tsige shi daga mukaminsa ba tare da ɓata lokaci ba domin shugaban ƙasa bai fi karfin doka ba,” in ji jam’iyyar.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya gamu da koma baya
A wani labarin, kun ji cewa wata kungiyar magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mai suna Tinubu Vanguard ta dawo daga rakiyarsa.
Kungiyar, wacce ke da dubban mambobi a jihohin Arewa 19 da Abuja ta bayyana cewa ta janye goyon bayan da take wa Shugaba Bola Tinubu saboda an yi watsi da ita.
Kungiyar ta kuma janye goyon bayanta ga jam’iyyar APC mai mulki, bisa dalilan watsi da ita, rashin karramawa da kuma wahalhalun da mambobinta ke fuskanta.
Asali: Legit.ng

