Zaben 2027: Shugaba Tinubu da APC Sun Gamu da Koma Baya kan Batun Tazarce

Zaben 2027: Shugaba Tinubu da APC Sun Gamu da Koma Baya kan Batun Tazarce

  • Wata kungiyar masoya mai goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta dawo daga rakiyarsa bayan zargin rashin kulawa
  • Kungiyar mai suna Tinubu Vanguard ta bayyana cewa ta ba gudunmawa sosai wajen tallata jam'iyyar APC gabanin zaben shekarar 2023
  • Sai dai, ta koka da cewa ba ta samu wani abin a zo a gani face watsi da ita da aka yi, wanda hakan ya sanya ta dauki matakin kama gabanta

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Ƙungiyar siyasa mai suna Tinubu Vanguard, wadda ta haɗa mambobi daga jihohi 19 na Arewa da Abuja, ta sanar da dakatar da dukkan ayyukanta na siyasa da kuma janye goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ta kuma janye goyon bayanta ga jam’iyyar APC mai mulki, bisa dalilan watsi da ita, rashin karramawa da kuma wahalhalun da mambobinta ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC

Shugaba Tinubu ya gamu da cikas kan zaben 2027
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ofis Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa shugaban kungiyar, Hon. Kamilu Abdullahi Abubakar Maiganji, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga mambobi da ’yan jarida.

Ya yi jawabin ne a wani taro da aka kira domin duba alakar kungiyar da gwamnatin da APC ke jagoranta.

Kungiyar ta taimaki Bola Tinubu da APC

Maiganji ya ce kungiyar Tinubu Vanguard ta taka muhimmiyar rawa wajen jawo goyon bayan jama’a a ga Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC kafin zaɓubbukan gama-gari na 2023.

Ya ce sun yi hakan ne ta hanyar shirye-shiryen rediyo da talabijin na dogon lokaci a jihar Kano da sauran sassan Arewacin Najeriya.

A cewarsa, wannan wayar da kan da suka yi ya taimaka wajen sauya ra’ayin jama’a, kara shigar al’umma cikin harkokin siyasa, tare da karfafa gwiwar mutane da dama da a baya ba sa shiga zaɓe su kaɗa kuri’a ga jam’iyyar a matakai daban-daban.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi gwamnoni 2 da suka san wahalar da ya sha kafin nasara a 2023

"Ba mu nemi kuɗi ba. Abin da kawai muka nema shi ne wurin taro, tsaro da masauki ga baki, amma babu ɗaya daga ciki da aka tanadar mana.”

- Hon. Kamilu Abdullahi Abubakar Maiganji

Kungiyar Tinubu Vanguard ta bar APC

Duk da wannan zargi na rashin tallafi, Maiganji ya ce mambobin ƙungiyar sun ɗauki nauyin kaddamar da ƙungiyar da kansu a Kano, taron da ya ce ya samu karɓuwa sosai a fadin Arewa.

Kungiya ta daina goyon bayan Shugaba Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter
"Daga yau, mun ajiye tsintsiya."

- Hon. Kamilu Abdullahi Maiganji

Sai dai ya jaddada cewa kungiyar ba ta yanke shawarar shiga wata jam’iyya ba har sai ta samu dandali da zai ga girman mutunci, gaskiya da ci gaban al’umma.

Shettima ya hango nasarar Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ja kunnen 'yan adawa kan zaben 2027.

Kashim Shettima ya bayyana cewa wauta ce babba wani dan adawa ya yi tunanin fafata da Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara.

Mataimakin shugaban kasar ya ce duk wani mai burin tsayawa takara da Shugaba Tinubu zai ba ta lokacinsa ne kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng