Manyan 'Yan Majalisun da Suka Fuskanci Barazanar Kiranye a 2025
FCT, Abuja - A shekarar 2025, an shigar da korafe-korafe kan wasu 'yan majalisu saboda yadda suke wakiltar mutanen da suka zabe su.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Wasu kungiyoyi sun yi barazanar yin kiranye ga 'yan majalisar wakilai da sanatoci wadanda ba su yarda da kamun ludayin wakilcinsu ba.

Source: Facebook
'Yan majalisun da suka samu barazanar kiranye
Legit Hausa ta yi duba kan manyan 'yan majalisun da suka fuskanci barazanar kiranye a shekarar 2025.
Mafi yawan lokuta ana yi wa 'yan majalisu barazanar kiranye ne saboda rashin gamsuwa da irin wakilcin da suke yi.
Sai dai, a wasu lokutan ana zargin cewa akwai siyasa a cikin barazanar kiranyen da ake yi ga wasu 'yan majalisu.
Duk da barazanar da aka yi, babu wani dan majalisa ko sanata da aka yi wa kiranye a shekarar 2025.
Ga jerin 'yan majalisun da suka fuskanci kiranye a 2025:
1. Sanata Lawal Adamu Usman
Kungiyar Kaduna Peace and Tranquility Forum (KPTF) ta yi barazanar yin kiranye ga Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Lawal Adamu Usman.
KPTF ta yi masa barazanar kiranye ne bisa zargin gaza tsayawa tsayin daka kan batutuwan ci gaba.
Ƙungiyar ta ce akwai matsalar rashin tsaro a mazabar Kaduna ta Tsakiya, amma ta zargi sanatan da rashin yin magana a kai a matsayinsa na mamba a majalisar dattawa ta 10.

Source: Twitter
Sun bayyana damuwarsu da cewa tsawon lokaci, ɗan majalisar bai yi magana kan matsalolin da ke addabar al’umma ba, kuma bai ja hankalin ayyukan gwamnatin tarayya zuwa jihar ba.
Sai dai Sanata Lawal Adamu Usman ya yi martani mai zafi ga ƙungiyar KPTF kan barazanar da ta yi na neman a dawo da shi daga majalisar dattawa bisa zargin rashin yin katabus, jaridar Premium Times ta kawo labarin.
Ya roƙi al’ummar Kaduna ta Tsakiya da kuma jama’ar jihar Kaduna gaba ɗaya da kada su yarda da karya da maganganun banza da KPTF ke yadawa, yana mai cewa babu ko ƙwayar gaskiya a cikinsu.
Sanata Lawal Usman ya kara da cewa barazanar yi masa kiranye ba ta dame shi ba ko kaɗan, inda ya buƙaci al’ummar Kaduna ta Tsakiya da su kwantar da hankalinsu.
2. Hon. Jide Ipinsagba
Wasu al’ummar mazabar Ondo ta Arewa sun yi barazanar kiranye ga Sanata Jide Ipinsagba, bisa zargin rashin katabus da kuma gazawa wajen aiwatar da muhimman ayyuka a mazabar.
Al’ummar, a karkashin kungiyar Ondo North Youth Alliance, sun zargi Sanata Ipinsagba da kin kula da ci gaban yankin da kuma bukatun jama’a tun bayan rantsar da shi a matsayin wakilinsu, jaridar gazettengr ta dauko labarin.
Sun kuma bayyana shirin fara tattara sa hannun masu kaɗa ƙuri’a domin ƙaddamar da tsarin kiranye.
Hakazalika sun zargi sanatan da rashin damuwa da karuwar matsalar rashin tsaro da ’yan daba ke haddasawa a Ondo ta Arewa, musamman a garin Owo.
3. Hon. Aliyu Sani Madakin Gini
Dan majalisa mai wakiltar Dala a majalisar wakilai, Aliyu Sani Madakin Gini, ya fuskanci barazanar kiranye.
Jaridar Daily Trust ta ce shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Lawan Hussaini Chediyar Yar Gurasa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya, suka jagoranci yunkurin yi wa Aliyu Sani kiranye.

Kara karanta wannan
Ba a gama murnar cin zabe ba, yan ta'adda sun sace mataimakin ciyaman da kansiloli 2

Source: Facebook
’Yan jam’iyyar NNPP a karamar hukumar Dala sun zargi Madakin Gini da aikata ayyukan cin amanar jam’iyya da kuma tafiyar Kwankwasiyya.
Shirin kiranyen ya biyo bayan sanarwar Madakin Gini ta ficewa daga tafiyar Kwankwasiyya, duk da cewa har yanzu mamba ne a jam’iyyar NNPP.
Sai dai shugaban bangaren jam'iyyar NNPP a Kano, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa, ya yi watsi da shirin yi wa dan majalisar kiranye, inda ya bayyana shi a matsayin abin dariya.
Ya ce ganin cewa an zabi Madakin Gini a karkashin jam’iyyar NNPP, ba za a iya aiwatar da irin wannan mataki ba tare da amincewarsa ba.
4. Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta fuskanci barazanar kiranye a shekarar 2025.
A ranar 24 ga Maris, 2025, wasu masu kaɗa kuri’a daga mazabar Kogi ta Tsakiya, a karkashin ƙungiyar Concerned Kogi Youth and Women, sun miƙa ƙorafi ga INEC a Abuja domin neman yin kiranye ga Sanata Natasha, rahoton TheCable ya tabbatar da hakan.
A cikin korafin da aka aika wa shugaban INEC na wancan lokacin, Mahmood Yakubu, mambobin kungiyar sun ce ba su gamsu da wakilcinta ba a majalisa, don haka suka bukaci hukumar ta fara tsarin dawo da ita.
Korafin ya samu sa hannun sama da masu kaɗa kuri’a 250,000 daga cikin fiye da 480,000 da aka yi wa rajista a Kogi ta Tsakiya, wanda ya cika sharadin kashi 50 cikin 100 da doka ta tanada domin fara aikin kiranye.
A martaninta, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi kakakkausar suka, inda ta bayyana shirin yi mata kiranye a matsayin aikin zamba da maguɗi.
5. Sanata Ede Dafinone
Sanata Ede Dafinone mai wakiltar mazabar Delta ta Tsakiya na daga cikin 'yan majalisun da suka fuskanci barazanar kiranye a 2025.
Kungiyar Nigeria Polling Unit Forum ta yi wa Sanata Ede Dafinone barazanar yi masa kiranye daga majalisar dattawa.
Shugaban kungiyar reshen jihar Delta, Nicholas Evwienure ya ce suna zargin Sanata Dafinone da gazawa wajen wakilci da rashin aiwatar da wasu ayyuka.
Natasha ta magantu kan shirin yi mata kiranye
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi tsokaci kan shirin yi mata kiranye daga majalisar dattawa.
Sanata Natasha ta bayyana cewa ba ta damu da ƙoƙarin da ake yi na ganin an raba ta da majalisar dattawa ba.
Ta bayyana cewa wasu mutane ne da ke adawa da ita suka dauki nauyin yunkurin ganin an yi mata kiranye.
Asali: Legit.ng



