Ana Wata ga Wata: An Cire Sule Lamido daga Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar PDP
- PDP reshen jihar Jigawa ta soki dakatar da Sule Lamido daga kwamitin amintattu na jam'iyyar, tana mai cewa matakin rashin adalci ne
- Shugaban PDP a Jigawa, Babandi Gumel, ya ce neman haƙƙin doka ba laifi ba ne, inda ya ce kotu ta taba yanke hukunci a madadin Lamido
- PDP Jigawa ta bukaci kwamitin ya janye dakatarwar nan take, ya nemi afuwa, tare da gina jam’iyya mai karfi bisa mutunta dattawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - PDP a Jigawa ta yi kakkausar suka kan matakin da kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar ya dauka na dakatar da tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido, daga kwamitin.
An ruwaito cewa a ranar Juma’a ne BoT na PDP ya sanar da dakatar da Lamido daga kwamitin bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa jam’iyya.

Source: Facebook
Sauran zarge-zargen sun haka da yin kalaman da suka tayar da husuma a lokacin rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta a baya-bayan nan, in ji rahoton Punch.
Lamido: PDP ta yi martani a Jigawa
Matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce a sassa daban-daban na jam’iyyar, musamman a Jigawa, inda aka ce hakan na iya kara rarrabuwar kai da raunana jam’iyyar gabanin zabuka masu zuwa.
A wata sanarwa da shugaban PDP na Jigawa, Babandi Gumel, ya sanya wa hannu, kuma aka fitar a Dutse, ya bayyana dakatarwar a matsayin rashin adalci da kuma matakin da bai dace ba.
Gumel ya ce matakin ya janyo damuwa da muhawara mai zurfi a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, yana mai jaddada cewa zargin da aka jingina wa tsohon gwamnan na halartar tarurrukan da ka iya barazana ga hadin kan jam’iyya ba su da tushe.
‘Yancin dan jam’iyya da hukuncin kotu
Shugaban PDP na Jigawa ya bayyana cewa neman ‘yancin doka da kundin tsarin mulki na jam’iyya ba zai taba zama laifi ko cin amanar jam’iyya ba.
Ya tunatar da cewa Lamido ya garzaya kotu ne bayan an hana shi damar sayen fom din tsayawa takarar kujerar shugaban jam’iyyar na kasa, in ji rahoton The Guardian.
“A fili Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci a madadinsa, inda ta hana PDP ci gaba da babban taronta har sai an tantance hakkin Lamido na tsayawa takara,” in ji Gumel.
Ya bayyana dakatarwar da aka yi wa Lamido a matsayin gaggawa da hukunci na son zuciya, yana mai cewa hakan raini ne ga tsarin shari’a da kuma hukuncin kotu.

Source: Original
Gudunmawar Lamido ga PDP
Gumel ya jaddada cewa Sule Lamido na daga cikin tubalan kafuwar PDP kuma ya kasance mai biyayya ga jam’iyyar tsawon rayuwarsa ta siyasa, ba tare da sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba.
“Ladabtar da irin wannan dattijo mai biyayya yana aika sakon da zai jefa firgici ga sauran mambobin jam’iyyar,” in ji Gumel.
Ya kara da cewa kundin tsarin PDP bai tanadi dakatar da mamba mai matsayin “mamban dindindin” kamar Lamido ba.
Jam’iyyar PDP a Jigawa ta bukaci BoT da ta gaggauta janye dakatarwar da aka kakaba wa Lamido ba tare da wani sharadi ba.
Sule Lamido ya fallasa makarkashiyar Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya soki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu game da adawa a Najeriya.
Sule Lamido ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati a matsayin makami domin danne dimokuraɗiyya.
Sule Lamido ya yi zargin cewa hukumomi kamar hukumar yaƙi da cin hanci da Rmrashawa ta EFCC suna zama makamin muzanta jiga-jigan adawa har su miƙa wuya.
Asali: Legit.ng


