Shan Suka kan Ziyarar Nnamdi Kanu Ta Sa Gwamna Ya Fadi Lokacin Daina Siyasa
- Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya sha suka kan ziyarar da ya kai wa Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali da ke Sokoto
- Alex Otti ya bayyana cewa bai kai ziyarar ba don burin neman mukamin shugaban kasa ko mataimakinsa a nan gaba
- Gwamnan ya kuma nuna cewa da zarar ya kammala jagorantar jihar Abia, zai ja baya daga dukkanin harkokin siyasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti, ya sake jaddada matsayarsa cewa zai yi ritaya daga siyasa bayan kammala wa’adinsa na gwamna.
Gwamna Otti ya bayyana cewa ba shi da burin tsayawa takarar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa ko sanata bayan ya bar mulki.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Gwamna Otti ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Disamban 2025 a gidan gwamnati da ke Umuahia yayin da yake martani kan wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta.
An taso Gwamna Otti a gaba kan Nnamdi Kanu
A cikin bidiyon wani mutum ya caccake shi kan ziyarar da ya kai wa Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali na Sokoto.
Mutumin ya yi zargin cewa gwamnan na da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban kasa bayan kammala wa’adinsa.
Gwamna Otti zai yi ritaya daga siyasa
Gwamnan, yayin da ya amince cewa sabanin ra’ayi wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya, ya ce kowa na da ’yancin ra’ayinsa, amma hakan ba lallai ne ya zama daidai ba, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
"Da farko dai, wannan shi ne kyawun dimokiraɗiyya. Mutane su rike ra’ayoyinsu, kuma muna girmama ra’ayoyin jama’a. Amma kasancewar ka na da ra’ayi daban ba yana nufin ka fi kowa gaskiya ba."
“Daya daga cikin abubuwan da ya ambata shi ne burina bayan zama gwamna. Na faɗa a baya, kuma ina sake faɗa a yau, cewa bayan na kammala aikin gwamna, zan yi ritaya."

Kara karanta wannan
Gwamna Fubara ya fadi biliyoyin da ya tarar a asusun Rivers bayan cire dokar ta baci
"Don haka ba ni da burin zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa. Haka kuma ba ni da burin zama sanata bayan na gama aikin gwamna."
“Na zo ne da wata manufa, kuma idan na kammala wannan manufa, zan bai wa matasa dama. Ya yi maganar da shugaban kasa dan Igbo. Ban ma fahimci ma’anar hakan ba."
"Don haka idan hujjarsa ta ta’allaka ne a kan wannan zato, to wannan zato ya rushe, domin ba zai gan ni a takardar zaɓe ba."
- Gwamna Alex Otti

Source: Facebook
Gwamnan Abia ya ba 'yan siyasa shawara
A cewar Gwamna Otti, yana da muhimmanci ga mai rike da mukamin siyasa ya san lokacin da ya dace ya yi ritaya, musamman bayan ya kammala aikin da aka dora masa.
"Idan ka yi abin da aka ɗora maka, dole ka san lokacin ja baya ka ba wasu dama. Mun ga wasu a nan da bayan sun yi gwamna, suka koma shugabancin ƙananan hukumomi. Wannan ba abin da muka zo yi ba ne. Ba mu dace da irin waɗannan abubuwa ba.”
- Gwamna Alex Otti
Gwamna Otti na son a saki Kanu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya fara shirin ganin an saki jagoran kungigar IPOB, Nnamdi Kanu.
Gwamna Alex Otti ya bayyana cewa tuni ya kaddamar da wata hanya ta siyasa da diplomasiyya domin ganin an saki Nnamdi Kanu.
Ya bayyana shirinsa na ganin an saki Nnamdi Kanu ya fara ne tun daga lokacin da aka fara shari'arsa kan zarge-zargen da ake yi masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

