Shugaban NNPP Ya Yi Bakar Addu'a ga Wadanda Suka Tsere daga Jam'iyya
- Jam’iyyar NNPP ta yi yi tir da 'ya'yanta da suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu, tana masu fatan tafiya mai cike da ƙalubale da rashin nasara
- Shugaban jam'iyyar na kasa, Ajuji Ahmed ne ya yi masu addua'a mara dadi, tare da jaddada cewa NNPP ta tsaya tsayin daka ba tare da rabuwar kai ba
- Ajuji Ahmed ya yaba da ayyukan gwamnatin NNPP a Kano tare da gargaɗi kan wani yunƙuri da ya ce ana yi na dora Najeriya a tsarin jam’iyya ɗaya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ajuji Ahmed, Shugaban NNPP na ƙasa, ya yi watsi da 'ya'yan jam’iyyar da suka sauya sheka zuwa wasu wadansu jam'iyyu a kasar nan.
Lamarin bai yi wa NNPP dadi ba, wanda ya sa Ahmed ya yi masu fatan tsiya, inda ya yi addu'ar su yi tafiyar siyasa mai cike da rudani da kalubale bayan rabuwa SU.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Shugaban NNPP ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 18 ga watan Disamba, 2025 yayin taron karo na goma na kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka gudanar a Abuja.
NNPP ta caccaki wadanda suka bar ta
A rahoton, Ajuji Ahmed ya siffanta masu sauya shekar a matsayin ‘yan tawaye, yana mai kira ga sauran 'yan jam’iyyar da su manta gaba ɗaya da hayaniyarsu.
A cewarsa:
“Ina roƙonku da ku manta gaba ɗaya da dabarun ‘yan tawaye da ke kiran kansu masu sauya sheka.”
Ya ƙara da cewa:
“Ubangiji Ya sa hanyarsu ta ci gaba da zama mai wuya.”
Ajuji Ahmed ya bayyana cewa idan 'ya'yan jam'iyyar sun zabi su bar nutusuwa su fada cikin wuta, babu dalilin da zai sa a yi masu fatan alheri.
Wannan magana ta nuna karara irin matsayar da NNPP ta ɗauka kan batun sauya sheka da kuma yadda take kallon tasirin hakan ga jam’iyyar.
Jam'iyyar NNPP ta fadi matsayarta
Ahmed ya jaddada cewa NNPP ta ci gaba da kasancewa a dunkule duk da ƙoƙarin wasu a waje na kawo mata cikas.
Ya ce jam’iyyar ba ta rarrabu zuwa ɓangarori da dama ba, kuma ba ta da shugabanni biyu ko uku. A cewarsa, ba a kwace jam’iyyar ba, ba a karya ta ba, kuma ba a sa ta zama marar tasiri saboda ba.
Ya ce:
“Mu ne NNPP, a hade mu ke, muna mai da hankali kan falsafarmu da manufofinmu na musamman.”
Shugaban jam’iyyar ya yaba da rawar da gwamnatin NNPP a jihar Kano ke takawa, yana yabon gwamna kan ayyukan da aka aiwatar a fannonin ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da bunƙasar ɗan Adam.

Source: Facebook
Ya ce waɗannan nasarori suna nuna cewa jam’iyyar na da hangen nesa da kuma ƙarfin aiwatar da manufofi masu amfani ga al’umma.
Ahmed ya kuma yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na kakaba tsarin jam’iyya ɗaya a ƙasar, yana mai cewa irin wannan shiri ba zai yi nasara ba.
'Yan NNPP sun bar jam'iyya a Kano
A baya, mun wallafa cewa jam’iyya mai mulkin Najeriya, APC ta karɓi 'ya'yan adawa 774 da suka sauya sheka daga NNPP a ƙaramar hukumar Rimin Gado ta jihar Kano bayan sun yi watsi da jam'iyyarsu.
Dr. Rabiu Sulaiman Bichi da ya jagoranci taron, ya bayyana sauyin shekar a matsayin shawara mai kyau, inda ita kuma APC ta jaddada cewa nasarorin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ne suka janyo wannan sauyi.
A jawabinsa, Bichi ya bayyana cewa waɗanda suka sauya shekar sun yi sa’ar ɗaukar shawara mai kyau a daidai lokacin da ƙasar ke buƙatar shugabanci nagari da jam’iyya mai hangen nesa.
Asali: Legit.ng


