Jam'iyyar PDP Ta Sake Rikicewa, Ƴan Majalisar Tarayya 4 Sun Sauya Sheka zuwa APC

Jam'iyyar PDP Ta Sake Rikicewa, Ƴan Majalisar Tarayya 4 Sun Sauya Sheka zuwa APC

  • 'Yan majalisar wakilai hudu daga Rivers sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a wani mataki na biyayya ga Gwamna Siminalayi Fubara
  • Wadanda suka sauya sheka sune ke wakiltar Port Harcourt 1, Ikwerre/Emuoha, Andoni/Opobo da Asari-Toru a majalisar wakilai
  • Sauyin shekar ya biyo bayan ficewar Gwamna Fubara da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar 18 daga PDP zuwa APC a kwanakin baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - ‘Yan majalisar wakilai hudu daga jihar Rivers sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC, lamarin da ke dagula lissafin PDP a jihar.

‘Yan majalisar da suka sauya sheka sun hada da Manuchim Umezuruike, wakilin Port Harcourt 1; Boniface Emerengwa, wakilin Ikwerre/Emuoha; Awake-Inombek Abiante, wakilin Andoni/Opobo; da kuma Boma Goodhead, wakilin Asari-Toru.

Wasu 'yan majalisar wakilan Rivers 4 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC
'Yan majalisar wakilai na gudanr da zaman majalisar da ke Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

'Yan majalisar PDP sun koma APC

Kara karanta wannan

Kakakin Majalisa na neman haddasa rigima a jam'iyyar APC kan tikitin zaben 2027

Channels TV ta rahoto cewa ‘yan majalisar da suka sauya shekar na daga cikin masu biyayya ga Gwamna Siminalayi Fubara, wanda shima ya fice daga PDP zuwa APC a makon da ya gabata.

Gwamna Fubara ya bayyana cewa ya fice daga PDP ne domin goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ba don goyon bayan shugaban kasa ba, da bai ci gaba da zama gwamna ba.

“Gaskiya ita ce, da ba don shugaban kasa ba, da Siminalayi Fubara ya zama tsohon gwamna. Ina tsaye tare da ku a yau ne saboda wannan goyon baya,” in ji Fubara.

Sauya shekar 'yan majalisar tarayyalr

Gwamnan ya ce ba zai ci gaba da goyon bayan shugaban kasa a boye ba, yana mai jaddada cewa dole ne ya fito fili ya bayyana cikakken goyon bayansa ta hanyar shiga APC.

“Ba za mu iya goyon bayan shugaban kasa a bayan fage ba. Don haka, mun yanke shawarar sauya sheka zuwa APC tare da dukkan wadanda suka sha wahala tare da ni,” in ji shi.

Ficewar ‘yan majalisar wakilai hudun ya zo ne kwanaki kadan bayan kakakin majalisar dokokin jihar Rivers, Martin Amaewhule, da wasu ‘yan majalisa 16 sun fice daga PDP zuwa APC a ranar 5 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya ba da tabbaci kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

‘Yan majalisar da suka sauya sheka sun bayyana cewa rikicin cikin gida da ya addabi PDP ne ya tilasta su barin jam'iyyar tare da shiga APC, in ji rahoton Punch.

Gwamna Fubara ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da ya sauya sheka daga PDP zuwa APC. Hoto: @SimFubaraKSC
Source: Facebook

Sunayen ‘yan majalisar da suka koma APC

Sauran ‘yan majalisar dokokin jihar da suka sauya sheka sun hada da mataimakin kakaki, Dumle Maol (Gokana), Major Jack (Akuku-Toru), Linda Stewart (Okrika).

Sauran sun hada da Franklin Nwabochi (Ogba/Egbema/Ndoni), Azeru Opara (Port Harcourt 3), Smart Adoki (Port Harcourt 2), Enemi George (Asari-Toru 2), da Solomon Wami (Port Harcourt 1).

Ragowar su ne; Igwe Aforji (Eleme), Tekena Wellington (Asari-Toru 1), Looloo Opuende (Akuku-Toru 2), Peter Abbey (Degema), Arnold Dennis (Ogu/Bolo), Chimezie Nwankwo (Etche), Gerald Oforji (Oyigbo) da Ofiks Kabang (Andoni).

Kara karanta wannan

PDP ta sake birkicewa, sanata ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Sabuwar rigima ta kunno kai Rivers

A wani labari, mun ruwaito cewa, wata sabuwar takaddama na kunno kai tsakanin bangaren Gwamna Siminalayi Fubara, da na ministan Abuja, Nyesom Wike.

Majiyoyi sun ce rigimar ta kunno kai ne kan wasu muhimman bangarori na yarjejeniyar sulhu da Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani a watannin da suka gabata.

An bayyana cewa ’yan majalisar dokokin Rivers suna shirin kin amincewa da duk wani kwamishina da ba ya goyon bayan bangaren Wike, da Gwamna Fubara zai gabatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com