Kakakin Majalisa na Neman Haddasa Rigima a Jam'iyyar APC kan Tikitin Zaben 2027

Kakakin Majalisa na Neman Haddasa Rigima a Jam'iyyar APC kan Tikitin Zaben 2027

  • Maganar da Kakakin Majalisar Dokokin Akwa Ibom ya yi game da tikitin takara a zaben 2027 ya fara tayar da kura a jam'iyyar APC mai mulki
  • Rt. Hon. Udeme Otong ya yi ikirarin cewa gaba daya tikitin 'yan Majalisa 26 yana hannunsa, babu wanda zai tsaya takara sai da amincewarsa
  • Wadannan kalamai ba su yi wa tsofaffin 'ya'yan APC dadi ba, inda wasu suka fara fitowa suna bayyana bacin ransu, tare da fatali da kalaman

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Kakakin Majaliaar Dokokin Jihar Akwa Ibom, Rt. Hon. Udeme Otong, ya tayar da kura da neman haddasa rikici APC watanni kadan bayan sauya sheka daga PDP.

Kara karanta wannan

'An riga an rubuta sakamakon zaben 2027," Kalaman kakakin majalisa sun tada ƙura

Kalaman da Hon. Otong ya yi kwanakin baya cewa gaba daya tikitin takarar 'yan majalisar jihar Akwa Ibom 26 na APC suna hannunsa sun haddasa ce-ce-ku-ce.

Udeme Otong.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom, Rt. Hon. Udeme Otong Hoto: Udeme Otong
Source: Twitter

Kalaman da ke neman hargitsa jam'iyyar APC

Daily Trust ta ruwaito cewa a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, Otong ya ce babu wani ɗan takara da zai samu tikitin jam’iyyar APC a 2027 sai da yardarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin majalisar ya yi wannan ikirari ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar mazabarsa da harshen Ibibio, inda ya ce duka tikitin yan majalisa 26 na karkashin ikonsa.

“Duka tikitin APC guda 26 na Majalisar Dokokin Jiharmu a zaɓen 2027 suna hannuna. Babu wani ɗan takara da zai samu tikitin jam’iyyar ba tare da amincewa ta ba,” in ji shi.

Wannan furuci ya jawo suka mai zafi daga wasu 'yan APC, musamman wadanda suka daɗe a cikinta tun kafin sauya sheƙar da Gwamna Umo Eno, Udeme Otong da wasu 'yan majalisa suka yi daga PDP zuwa APC.

'Yan APC sun dura kan kakakin Majalisa

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya ba da tabbaci kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Kungiyar 'yan APC a Akwa Ibom ta yi Allah-wadai da kalaman Kakakin Majalisar, tana mai kiran su da “yunkurin tada hankali kuma sun cin karo da dimokiraɗiyya."

A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Iniobong John, ya fitar a birnin Uyo, ya ce ’yan takarar APC a zaɓen 2027 za su fito ne ta hanyoyin da kundin tsarin jam’iyya ya tanada, ba ta furucin mutum ɗaya ba.

Udeme Otong.
Kakakin Majalisar Dokokin Akwa Ibom, Rt. Hon. Udeme Otong da tambarin APC Hoto: Udeme Otong
Source: Facebook

Ya jaddada cewa ba Kakakin Majalisar ba, ko ma waye, babu wani mutum guda ɗaya da ke da ikon tantance ko raba tikitin jam’iyyar APC da zaben da ke tafe, in ji rahoton Punch.

John ya jaddada cewa wannan iko gaba daya yana hannun jam’iyyar APC, kuma ana aiwatar da shi ta tsare-taaren jam’iyyar da doka ta amince da su.

Sanatan Kaduna ya koma jam'iyyar APC

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, Sunday Marshall Katung, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta wasikar sauya shekar sanatan a zaman yan majalisar na ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

"Ba zan taba komawa APC ba," Sanata ya yi kaca kaca da gwamnoni 6 a Najeriya

Sanata Marshall Katung ya ce PDP ta shiga tsaka mai wuya na rarrabuwar kai, tare da cewa jam’iyyar ba ta dace da muradun masu kada kuri’a a mazabarsa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262