Abin da Ya Sa Ake Ganin Ya Kamata a Daure Kusan duka Ministocin Buhari a Gidan Yari

Abin da Ya Sa Ake Ganin Ya Kamata a Daure Kusan duka Ministocin Buhari a Gidan Yari

  • Alwan Hassan ya yi kaca-kaca da kusan duka ministocin da suka yi aiki karkashin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
  • Jigon APC ya bayyana cewa kamata ya yi zuwa yanzu sama da kaso 90 na ministocin marigayi Buhari na daure a gidan gyaran hali
  • Ya ce ba a taba samun wani lokaci da ake sakar wa kowane minista kasafin kudi ba tare da sanya masa iso ba kamar lokacin Buhari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani jigo a jam’iyyar APC, Alwan Hassan, ya yi ikirarin cewa kashi 95 cikin 100 na ministocin da suka yi aiki da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba mutanen kirki ba ne.

Alwan Hassan ya yi ikirarin cewa kamata ya yi a ce an daure 95% na ministocin Buhari a gidan yari zuwa yanzu, saboda yadda ake zargin mulkinsu cike yake da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

"A bar shi ya huta": Nasir El Rufa'i ya yi magana game da littafi kan Buhari

Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto: @MBuhari
Source: Facebook

Jigon na APC ya bayyana wannan zargi ne a wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, wanda aka watsa a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ya kamata a daure ministocin Buhari' - Alwan

Da aka tambaye shi game da binciken da ake yi kan wasu jami’an gwamnatin Buhari, ciki har da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, Alwan Hassan ya ce:

“Kamata ya yi zuwa yanzu, kashi 95 cikin 100 na ministocin da suka yi aiki a karkashin Buhari su na daure a gidan yari.
“Ba a taba samun wani lokaci da aka bai wa ministoci cikakken ‘yanci ba tare da kulawa ko sa ido ba kamar shekaru takwas na mulkin Buhari.”
“An ce shi kansa tsohon shugaban kasar ya taba gaya musu su tanadi hujjojinsu, domin wata rana za a bukaci su yi bayani. Watakila ya riga ya fahimci abin da suke aikatawa.”

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Hassan ya yi ikirarin cewa cin hanci da rashawa ya yi katitu a lokacin mulkin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Akwai miniatoci nagari a mulkin Buhari?

Sai dai ya amince cewa akwai ‘yan kalilan daga cikin jami’an gwamnatin da ba su shiga irin wadannan laifuffuka ba, in ji Daily Post.

“Wadannan mutane na gari ba su wuce kashi 5 cikin 100 ba. Akwai na kirki, amma kadan ne sosai,” in ji shi.
Buhari.
Tsohon shugaban Najeriya da Allah ya yi wa rasuwa a 2025, Muhammadu Buhari Hoto: Bashir Ahmad
Source: Getty Images

Hassan ya jaddada cewa rashin sa ido da kulawa ya taimaka wajen tabarbarewar lamarin, inda ya bayyana wancan lokaci a matsayin “kowa ya yi abin da ya ga dama.”

“Ba a taba samun wani lokaci da ake sakin kasafin kudi 100% ba tare da tsoma bakin fadar shugaban kasa ba kamar a lokacin Buhari. An bai wa ministoci cikakken iko. Suna yin abin da suka ga dama," in ji shi.

Yadda aka danne Monguno a mulkin Buhari

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Babagana Monguno, ya tuna matsalolin da ya fuskanta a gwamnatin baya.

Kara karanta wannan

Tonon silili: Aisha Buhari ta fadi kuskuren da mijinta ya yi a lokacin mulkinsa

Monguno ya bayyana cewa masu karfin iko da ke juya gwamnati a hannunsa, su ne suka hana ofishinsa yin katabus a mulkin marigayi Muhammadu Buhari.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce hana ofishinsa kudade ya raunana tsarin tsaron kasa, tare da makantar da gwamnati wajen gano barazana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262