ADC Ta Samu Karuwa, Sanata Mai Ci Ta Sanya Lokacin Yin Rajista a Jam'iyyar
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya za ta samu sanata mai ci wadda za ta yi rajista domin zama daya daga cikin mambobinta
- Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, Ireti Kingibe, ta sanya lokacin da za ta yi rajista da jam'iyyar ADC a hukumance
- Ireti Kingibe za ta yi hakan ne bayan ta sauya sheka daga jam'iyyar LP wadda ta lashe kujerar Sanata a zaben shekarar 2023 da ya gabata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, Ireti Kingibe, za ta yi rajista da jam'iyyar ADC.
Sanata Ireti Kingibe ta ce za ta yi rajista a hukumance a jam’iyyar ADC a ranar Alhamis, 18 ga watan Disamban 2025.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mai ba ta shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kennedy Mbele, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Ireti Kingibe ta fice daga LP
A watan Yuli, Kingibe ta sanar da ficewarta daga jam’iyyar Labour Party (LP) zuwa ADC, a matsayin wani shiri gabanin babban zaɓen 2027.
Sanatar ta ce sauya shekar da ta yi mataki ne da ta yi tunani sosai a kai, kuma za ta kammala shi a hukumance tare da gudanar da gagarumin taro.
Sanata Ireti ta ce za a gudanar da rajistar da ƙarfe 10:00 na safe a hedkwatar jam’iyyar ADC ta kasa da ke Wuse, Abuja.
Sanarwar ta ce wannan mataki ya tabbatar da ficewar Kingibe daga jam'iyyar LP gaba ɗaya, tare da nuna cewa rajistar za ta shigar da ita ADC a hukumance, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
Ireti Kingibe za ta shirya gangami
Ana sa ran manyan jami’an ADC, ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja da za a yi a ranar 21 ga watan Fabrairun 2026, magoya bayan jam’iyyar da kuma ’yan jarida za su halarci taron.
“Matakin jarumta da Kingibe ta ɗauka na shiga ADC ya sa ta zama sanata mai ci a halin yanzu guda ɗaya tilo a sabuwar jam’iyyar adawa mai tasowa, ADC."
- Kennedy Mbele

Source: Twitter
Sanarwar ta kuma bayyana kwarewa da tarihin aikin Sanatar a matsayin babban abu mai matuƙar amfani a kowanne fagen siyasa a duniya.
A ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2025, majalisar dattawa ta ƙi amincewa da wani kudiri da Sanata Ireti Kingibe ta gabatar, wanda ke neman majalisa ta shiga tsakani kan wasu manyan matsalolin da suka shafi mulki da ke addabar Abuja.
Abin da ADC ta ce kan tafiyar Atiku da Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi magana kan yiwuwar tafiya tare tsakanin Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi.
Jam'iyyar ADC ta nuna damuwa kan yadda Atiku Abubakar da Peter Obi ba su aiki tare domin tunkarar zaɓen 2027.
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya yi amanna cewa jam’iyyar na cikin damuwa dangane da rashin haɗin gwiwa tsakanin Peter Obi da Atiku.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

