Kanin Abubakar Malami Ya Samu Mukami Mai Girma a Gwammati Awanni 24 da Shiga APC
- Kanin tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya samu mukami mai muhimmanci a gwamnatin jihar Kebbi
- Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da nadin Almustapha Malami a matsayin sabon shugaban hukumar KEBGIS kuma zai fara aiki nan take
- Wannan nadi na zuwa ne kasa da wanni 24 bayan 'dan uwan Malami ya shiga APC kuma ya ayyana goyon bayansa ga Gwamna Nasir Idris
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Siyasar jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma na ci gaba da daukar hankali musamman tsakanin Gwamna Nasir Idris da tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami.
Kasa da sa'o'i 24 bayan ya shiga APC tare da goyon bayan kudirin tazarcen Gwamna Nasir Idris, 'dan uwan Abubakar Malami ya samu mukami a gwamnatin jihar Kebbi.

Source: Twitter
Kanin Malami ya samu mukami a Kebbi
Tashar Channels tv ta ruwaito cewa Gwamna Nasir ya amince da nadin Almustapha Malami a matsayin shugaban hukumar kula da filayen Kebbi (KEBGIS).
Almustapha dai kani ne ga tsohon Antoni-Janar na Tarayya da Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), wanda ke fuskantar binciken hukumar EFCC a baya-bayan nan.
An sanar da nadin dan uwan Malami ne a cikin wata takarda da Shugaban Ma’aikata na Jihar Kebbi, Malami Shekare, ya sanya hannu, wadda aka fitar a ranar Talata.
Gwamnatin Kebbi ta taya Almustapha Malami murna
A cikin takardar, Malami Shekare ya taya wanda aka nada murna, sannan ya bukaci ya nuna jajircewa, himma, da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukansa, bisa ka’idoji da manufofin gwamnatin jihar Kebbi.
“Gwamnati na sa ran za ka yi amfani da dukkan kwarewarka domin tabbatar da an tafiyar da harkokin gudanarwar tsarin bayanai na jiha da inganta harkar kula da filaye.”
A cewar sanarwar da gwamnatin Kebbi ta raba wa manema labarai, nadin zai fara aiki ne nan take.
Muhimmancin hukumar KEBGIS a Kebbi
KEBGIS wata hukuma ce mai muhimmanci wadda ke da alhakin tafiyar da harkokin filaye, tsara taswira, da kuma hada bayanan kowane fili ta intanet a Jihar Kebbi.
Wannan ya sanya mukamin shugaban hukumar KEBGIS ya zama mai matukar muhimmanci a tsarin mulki da ci gaban jihar Kebbi.

Source: Facebook
Nadin 'dan uwan tsohon ministan ya jawo magana tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin an yi shi ne bisa dalilan siyasa, yayin da wasu ke ganin an yi shi ne a matsayin lada ga biyayya ga jam’iyyar gwamnati.
Sai dai har yanzu, gwamnatin Kebbi ba ta mayar da martani kan wannan muhawara da mutane ke yi game da lokacin da aka yi nadin ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Malami ya fayyace binciken da EFCC ke masa
A wani rahoton, kun ji cewa Abubakar Malami ya ce tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa ta takaita ne kan batun aikin dawo da kudaden tsohon Shugaba Sani Abacha.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi
Tsohon Ministan ya ce babu wata hukuma ta tsaro ko leƙen asiri a Najeriya ko waje da ta taɓa zarginsa da daukar nauyin ta’addanci ko mallakar asusun bankuna da yawa.
Malami SAN ya ce EFCC ta gayyace shi ne kawai domin ya fayyace batun dala miliyan 310 na kudin Abacha da aka dawo da su a zamanin gwamnatin Muhammadu Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

