Manyan Badakalolin Siyasa 5 da Suka Faru a Shekarar 2025 a Najeriya

Manyan Badakalolin Siyasa 5 da Suka Faru a Shekarar 2025 a Najeriya

  • Shekarar 2025 ta girgiza siyasar Najeriya, manyan ‘yan siyasa, musamman daga APC, suka shiga zarge-zargen badakala da suka dauki hankali
  • Zarge-zargen sun shafi amfani da takardun bogi, zargin cin zarafin mata sai kuma karkatar da dukiyar gwamnati da sauransu
  • Nan da yan kwanaki kadan, za a shiga sabuwar shekarar 2026 wanda zai rage saura shekara daya a gudanar da zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shekarar 2025 ta zo da cakudaddun labarai a siyasar Najeriya, inda wasu ‘yan siyasa suka samu nasarori, yayin da wasu kuma suka fada cikin badakala.

Kamar yadda aka saba, sunayen manyan ‘yan siyasa da tsofaffin jami’an gwamnati sun mamaye kafafen yada labarai sakamakon zarge-zargen rashin da’a.

Wasu badakalolin siyasa da suka faru a 2025
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Badakalolin siyasa da suka faru a 2025

Rahoton Punch ya ce an samu wasu yan siyasa da dama ciki har da wadanda suka fito daga jam'iyyar APC da rashin da'a.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama mutane 627, a jiha 1 kadai an kwato bindigogin AK 47 guda 27

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattara wasu daga cikin manyan badakalar siyasa da suka girgiza Najeriya a shekarar 2025.

1. Badakalar takardun karatun Uche Nnaji

A watan Oktobar 2025, Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa bayan bullar zargin cewa ya kirkiri takardun shaidar karatu na bogi.

Rahotanni sun ce wani binciken jarida ya gano cewa Nnaji ya mika takardun bogi ga Shugaba Bola Tinubu lokacin nadinsa a 2023.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar da murabus din Nnaji ta shafin X, inda ya ambato ministan yana cewa yana fuskantar barazana da bakar siyasa daga abokan hamayya.

Duk da haka, Nnaji ya musanta zargin, yana mai jaddada cewa ya kammala karatu a Jami’ar UNN ta Nsukka (UNN).

Minista ya yi murabus kan takardun bogi
Tsohon minista, Uche Nnaji daga Enugu. Hoto: Hon. Uche Nnaji.
Source: UGC

2. Rikicin Godswill Akpabio da Natasha Akpoti-Uduaghan

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar da koke a Majalisar Dattawa tana zargin shugaban majalisar, Godswill Akpabio, da cin zarafinta ta hanyar neman lalata.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu na amfani da EFCC wajen kama 'yan adawa a Najeriya?

Daga bisani, majalisar ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida, lamarin da ya jawo maganganu da zarge-zarge tsakanin al'umma.

Akpabio ya musanta zargin a zaman majalisar dattawa a watan Maris din shekarar 2025, yana cewa:

“A kowane lokaci, ban taba cin zarafin wata mace ba.”

Bayan kammala wa'adin dakatarwar da aka yi mata, Natasha ta koma majalisar dattawa bayan an dai kai ruwa rana da 'yan kwanaki.

An gwabza rigima tsakanin Natasha da Akpabio
Sanata Natasha Akpto da Godswill Akpabio. Hoto: The Nigeria Senate.
Source: Facebook

3. Zargin EFCC kan Timipre Sylva

A watan Nuwamba, Hukumar EFCC ta fitar da sammacin kama tsohon ministan man fetur, Timipre Sylva.

Hukumar ta zarge shi da karkatar da kusan dala miliyan 15 da aka ware domin gina matatar mai.

EFCC ta wallafa sanarwar neman sa a shafukan sada zumunta, tana rokon duk wanda ke da bayanin inda yake ya tuntube ta.

Sylva ya mayar da martani, inda ya zargi EFCC da kai farmaki ba bisa ka’ida ba a gidansa da ke Maitama, Abuja.

Hakan ya biyo bayan zarginsa da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu wanda ya musanta.

Kara karanta wannan

"A bayyane yake": An hango abin da Tinubu zai yi wa Shettima a zaben 2027

Zarge-zarge sun yi yawa kan Timipre Sylva
Tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva. Hoto: Timipre Marlin Sylva.
Source: Facebook

4. Zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu

A watan Oktobar 2025, an yi ta yada cewa wasu manyan sojoji sun yi yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu daga mulki, cewar Vanguard.

Daga bisani, an samun bayanai kan sojoji 16 da ake zargin su na tsare kan jita-jitar shirin juyin mulki a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun kunshi jami'an rundunar sojojin kasa 14 da jami'i daya daga rundunar sojojin ruwa da sojan sama daya.

Hedkwatar tsaro dai ta musanta batun juyin mulkin tun farko da ake ta yadawa, inda ta ce ta tsare sojojin ne kan wasu dalilai daban.

An nade wasu sojoji kan zargin yunkurin juyin mulki
Ministan tsaro, Christopher Musa da Bola Tinubu. Bayo Onanuga, HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

5. Digirin Dakta na Rarara ya jawo magana

Mawakin siyasa a Arewacin Najeriya ya jawo maganganu bayan sanar da samun girmamawa da aka yi masa ta digirin digirgir.

An gudanar da bikin karrama mawaki Dauda Rarara a Abuja, inda jami’ar European American ta ba shi lambar yabo.

Kara karanta wannan

Sababbin jakadu: Mutane 5 da Tinubu ya nada da suka fuskanci manyan zarge zarge

Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da Gwamnan Katsina, ministoci da kuma amaryar Rarara watau Aisha Humairah.

Samun girmamawar da mawakin APC ya samu ya bar baya da kura inda wasu ke ganin abin ya zama siyasa saboda kwata-kwata bai cancanta ba.

Haka zalika yunkurin nazarin wakokinsa ya bar baya da kura a jami'ar FUDMA a Dutsin Ma, jihar Katsina kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Martanin Rarara kan ba shi digirin Dakta

Rarara ya yi martani game da lamarin, inda ya yi godiya bisa girmama shi da digirin Dakta daga jami’ar, duk da ce-ce-ku-ce kan haka.

Mawakin ya musanta zargin biyan kudi don samun digirin, inda ya ce karamawar ta biyo bayan gudunmawarsa ga al’umma, yaren Hausa da siyasa.

A cewarsa, jami’ar ta yaba masa ne saboda kokarinsa wajen kula da jama’a da rawar da ya taka a siyasa da bunkasa harshen Hausa.

An girmama Rarara da digirin digirgir
Mawaki a Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara. Hoto: Rabiu Garba Gaya.
Source: Facebook

Malami ya yi zarge-zarge kan shugaban EFCC

Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan Shari'a a mulkin Muhammadu Buhari, Abubakar Malami SAN, ya koka kan ci gaba da tsare shi da hukumar EFCC ke yi.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Malami ya yi zargin cewa shugaban EFCC ya kullace shi saboda wasu abubuwa da suka faru a baya.

Tsohon Ministan ya ba hukumar EFCC wa'adin lokacin da za ta sake shi ko kuma ta gurfanar da ita a gaban kotu domin neman hakkinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.