"Ba Za Su Iya ba": Sanata Ya Karya Lagon Masu Goyon bayan Tinubu

"Ba Za Su Iya ba": Sanata Ya Karya Lagon Masu Goyon bayan Tinubu

  • Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi tsokaci kan goyon bayan da wasu 'yan siyasa ke nunawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Enyinnaya Abaribe ya bayyana cewa 'yan siyasa ba su karfin da za su iya fitowa su nemar masa kuri'a a yankunan da suka fito
  • Sanatan ya bayyana abin da zai faru gare su idan suka fito tallata shugaban kasar ga mutanen yankunan su a zabe mai zuwa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata Enyinnaya Abaribe, mai wakiltar Abia ta Kudu, ya yi magana kan 'yan siyasar da ke nuna goyon baya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Abaribe ya yi ikirarin cewa da dama daga cikin ’yan siyasar da ke bayyana goyon baya ga Shugaba Tinubu, ba za su iya fita fili a garuruwansu su nemar masa kuri’a ba.

Kara karanta wannan

"Bai ci zabe ba a 2023": Sanata ya hango makomar Tinubu a zaben 2027

Sanata Abaribe ya soki masu goyon bayan Tinubu
Sanata Enyinnaya Abaribe da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @PO_GrassRootRM
Source: Twitter

Sanata Abaribe ya fadi hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Enyinnaya Abaribe ya yi watsi da abin da ya kira nuna karfin jam’iyya mai mulki ta APC a jihohi, yana mai cewa hakan bai dace da ra’ayin jama’a ba.

Abaribe: "Talakawa za su zama raba gardama"

Da yake tuno wata tattaunawa game da yadda APC ke rike da matakai daban-daban na gwamnati, sanatan ya ce ainihin gwajin goyon bayan siyasa na faruwa ne a matakin tushe, wato a tsakanin talakawa.

Ya ambaci wata tambaya da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya taba yi domin karfafa hujjarsa.

“Ni daga Aba na fito. Ina tattaunawa ne cewa APC na da wannan gwamnati da wancan gwamnati, mutane kuma sun fara nuna damuwa. Sai na tambayi daya daga cikinsu wata tambaya."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi

"A gaskiya ma, tsohon gwamna Peter Obi ne ya taba yin wannan tambayar. Ya ce shin Abaribe da ke nan, zai iya zuwa kasuwar Ariaria ya ce musu su zabi Bola Tinubu? Ba zai iya ba.”
“Yawancin mutanen da ke cewa suna goyon bayan Tinubu ba za su iya komawa gidajensu su fada hakan ba. Ba za su iya ba, me ya sa? Domin za a jifesu da duwatsu idan suka je suna fadin irin wannan magana."

- Sanata Enyinnaya Abaribe

Abaribe ya ce Tinubu zai sha kashi a zaben 2027
Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu, Enyinnaya Abaribe Hoto: @PO_GrassrootRM
Source: Twitter

Abaribe ya hango faduwar Tinubu a 2027

Sanatan ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Tinubu zai sha kaye a zaben gama-gari na shekarar 2027, yana mai jaddada cewa shugaban kasar bai samu sahihiyar nasara a zaben 2023 ba.

“Tinubu zai fadi a zaben 2027; bai taba lashe zaben 2023 ba."
“Za mu hadu da shi a filin zabe, sannan mu ga yadda zai hada wani tsari da zai ba shi nasara a karo na biyu, hakan ba zai yi aiki ba.”

- Sanata Enyinnaya Abaribe

Tinubu ya yi ta'aziyyar mataimakin gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan rashin da aka samu a jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

'Ko $1bn aka ba ni, ba zan shiga sabgar ba': Malamin addini ya tsinewa siyasa

Shugaba Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.

Mai girma Tinubu ya jajantawa gwamnati, al'ummar jihar Bayelsa kan rasuwar Lawrence wanda ya bayyana a matsayin jajirtaccen shugaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng