Ra'ayi Riga: Kanin Malami Ya Juya Masa Baya, Ya Goyi bayan Tazarcen Gwamnan Kebbi a 2027

Ra'ayi Riga: Kanin Malami Ya Juya Masa Baya, Ya Goyi bayan Tazarcen Gwamnan Kebbi a 2027

  • Siyasar jihar Kebbi ta dauki sabon salo bayan da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya bayyana aniyarsa ta yin takara a zaben 2027
  • Sai dai, Malami ya samu koma baya daga cikin gida bayan da kaninsa ya fito ya nuna goyon baya ga Gwamna Nasir Idris na jam'iyyar APC
  • Almustapha Malami ya bayyana dalilan da yake ganin ya kamata su sanya Gwamna Nasir Idris ya sake komawa kan kujerarsa a zabe mai zuwa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Almustapha Malami, kanin tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana goyon bayansa ga gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris.

Al-Mustapha Malami ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen Gwamna Nasir Idris a zaben shekarar 2027.

Gwamnan Kebbi ya samu goyon baya daga kanin Malami
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi da Abubakar Malami Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu, Abubakar Malami, SAN
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Almustapha Malami ya bayyana hakan ne yayin wani taro a Birnin Kebbi ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi a Sokoto, mataimakin kwamishinan ƴan sanda ya bar duniya

Meyasa kanin Malami ke goyon bayan gwamnan Kebbi?

Almustapha Malami ya danganta goyon bayansa da tarin nasarorin da gwamnatin Nasir Idris ta cimma cikin shekaru biyu na farko.

Ya bayyana cewa hakan ne ya sa ya yanke shawarar mara wa jam’iyya mai mulki ta APC baya, jaridar Leadership ta dauko labarin.

Matakin ya jawo hankalin masu sharhi, la’akari da cewa ana ganin cewa babban yayansa kuma tsohon AGF, yana da burin tsayawa takarar gwamna a shekarar 2027, kuma tuni ya fice daga APC zuwa jam’iyyar ADC.

Masu sharhin siyasa sun bayyana goyon bayan Almustapha Malami ga Gwamna Nasir Idris a matsayin abin mamaki, musamman duba da dadaddiyar hamayya ta siyasa da ke tsakanin gwamnan da babban yayansa, wadda ta sha samun musayar kalamai masu zafi a baya.

“Ko muna so ko ba mu so, Gwamna Nasir Idris ya sauya fasalin Birnin Kebbi tare da kai babban birnin jihar matsayin da ya dace."

Kara karanta wannan

'Yana kan daidai': Gumi ya goyi bayan Matawalle, ya fadi tasirinsa a Zamfara

“Idan aka sake zabensa a 2027, jihar Kebbi za ta samu cigaba mai girma fiye da yadda ake gani a yanzu, musamman a bangaren bunkasar birane.”

- Almustapha Malami

Kanin Malami ya goyi bayan tazarcen Gwamna Nasir Idris
Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami, SAN
Source: Twitter

Almustapha Malami bai tsoron komai

Ya jaddada cewa ya dauki wannan matsaya ne da radin kansa ba tare da matsin lamba daga ko ina ba, yana mai cewa babu wata tsoratarwa ko barazana da za ta hana shi goyon bayan tazarcen gwamnan.

“Na shiga wannan tafiya ne da zuciya daya da kuma kwanciyar hankali. Babu abin da zai hana ni mara wa gwamnati baya wadda ke cika alkawuran da ta dauka wa al’umma."

- Almustapha Malami

Malami ya jefi shugaban EFCC da zargi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malam, ya yi zarge-zarge kan shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Abubakar Malami ya zargi shugaban na EFCC da kullatarsa a zuciya saboda wasu abubuwa da suka faru a lokacin da yake jagorantar ma'aikatar Shari'a a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

Tsohon Ministan ya bukaci ahugaban na EFCC ya janye hannunsa daga binciken da ake yi masa domin ba zai yi masa adalci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng