Cikakken Jerin Gwamnonin Najeriya da Jam'iyyunsu a Watan Disamban 2025
- Jam’iyyar APC ta kara tabbatar da cikakken ikonta a yawancin jihohin Najeriya, inda take rike da kujerun gwamnoni 27 a faɗin yankuna daban-daban na kasar
- Jam’iyyun adawa sun ci gaba da kasancewa da karamin tasiri amma mai muhimmanci, inda PDP ke mulkin jihohi biyar, yayin da wasu jam’iyyu ke da guda uku
- Rarrabuwar gwamnonin ya nuna banbancin ra'ayin siyasa, domin kuwa har yanzu akwai jihohin da ke karkashin kananan jam'iyyu irinsu LP, APGA da NNPP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja, FCT - Yanayin siyasar Najeriya zuwa tsakiyar watan Disamba na shekarar 2025 ya nuna karkata sosai ga jam’iyyar APC mai mulki, wadda ke rike da mafi yawan gwamnatocin jihohi a faɗin kasar.
Rarraba gwamnonin bisa jam’iyya ya nuna yadda sakamakon zaɓuɓɓukan baya-bayan nan da kuma sauye-sauyen kawancen siyasa a matakin jihohi suka kasance.

Kara karanta wannan
Shugaban Ƙasa, gwamnoni da ciyamomi sun raba Naira tiriliyan 1.92 a watan Nuwamba

Source: Twitter
Jam'iyyar APC na da mafi yawan gwamnoni
Wani amfani da shafin X mai suna @ImranMuhdz, ya sanya cikakken jerin gwamnonin Najeriya da jam'iyyun da suka fito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da gwamnoni 27, APC ta kasance jam’iyya mafi karfi kuma mafi yawan gwamnoni a cikin jihohi 36 na Najeriya.
Ikon APC ya shafi muhimman cibiyoyin tattalin arziki da kuma jihohi masu muhimmancin siyasa, ciki har da Legas, Ribas, Delta da Kaduna.
Wannan faɗaɗɗen tasiri ya sanya jam’iyyar a matsayi mai karfi gabanin zaɓuka masu zuwa da kuma tattaunawar mulki tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi.
Jam'iyyar APC ta kasance da mafi yawan gwamnoni tun bayan zaben shekarar 2023 da aka gudanar a cikin jihohi 28 na Najeriya.
Hakazalika, jam'iyyar APC ta yi nasara a wasu zabubbukan gwamnoni da aka gudanar a jihohin Kogi da Edo.
Daga baya wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyun adawa sun rika yin tururuwa zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Jam'iyyun adawa na da tsirarun gwamnoni
Jam’iyyar PDP ta biyo baya a matsayi na biyu, inda take da gwamnoni a ƴan jihohi kaɗan na Najeriya.
Jaridar The Punch ta ce ya zuwa watan Disamban 2025, gwamnoni shida suka rage a cikin jam'iyyar PDP, wannan adadin ya ragu zuwa biyar biyo bayan sauya shekar da gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya yi zuwa APC.
Tun bayan zaben shekarar 2023, gwamnoni shida ne suka fice daga jam'iyyar PDP, inda biyar daga cikinsu suka koma APC, yayin da daya kuma ya koma jam'iyyar Accord Party.
Duk da cewa PDP ta ci gaba da kasancewa mai tasiri a wasu sassan Arewa Maso Gabas, Arewa Ta Tsakiya da Kudu Maso Yamma, raguwar yawan jihohin da take mulki na nuna kalubalen da take fuskanta wajen dawo da ƙarfinta tun bayan zaɓukan gama-gari na karshe.

Source: Twitter
A kasa akwai cikakken jerin gwamnonin Najeriya bisa jam’iyyun siyasa zuwa ranar 17 ga watan Disamba, 2025.
Jam'iyyar APC - Gwamnoni 27
- Jihar Akwa Ibom: Umo Eno
- Jihar Bayelsa: Douye Diri
- Jihar Benue: Hyacinth Alia
- Jihar Borno: Babagana Umara Zulum
- Jihar Cross River: Bassey Otu
- Jihar Delta: Sheriff Oborevwori
- Jihar Ebonyi: Francis Nwifuru
- Jihar Edo: Monday Okpebholo
- Jihar Ekiti: Biodun Oyebanji
- Jihar Enugu: Peter Mbah
- Jihar Gombe: Muhammad Inuwa Yahaya
- Jihar Imo: Hope Uzodimma
- Jihar Jigawa: Umar Namadi
- Jihar Kaduna: Uba Sani
- Jihar Katsina: Dikko Umar Radda
- Jihar Kebbi: Nasir Idris
- Jihar Kogi: Usman Ododo
- Jihar Kwara: Abdulrahman Abdulrazaq
- Jihar Legas: Babajide Sanwo-Olu
- Jihar Nasarawa: Abdullahi Sule
- Jihar Neja: Mohammed Umar Bago
- Jihar Ogun: Dapo Abiodun
- Jihar Ondo: Lucky Aiyedatiwa
- Jihar Rivers: Siminalayi Fubara
- Jihar Sokoto: Ahmad Aliyu
- Jihar Taraba: Agbu Kefas
- Jihar Yobe: Mai Mala Buni
Jam'iyyar PDP - Gwamnoni 5
- Jihar Adamawa: Ahmadu Umaru Fintiri
- Jihar Bauchi: Bala Mohammed
- Jihar Oyo: Seyi Makinde
- Jihar Plateau: Caleb Mutfwang
- Jihar Zamfara: Dauda Lawal
Jam'iyyar Accord Party - Gwamna 1
1. Jihar Osun: Ademola Adeleke
Jam'iyyar Labour Party (LP) - Gwamna 1
1. Jihar Abia: Alex Otti
Jam'iyyar APGA - Gwamna 1
1. Jihar Anambra: Charles Chukwuma Soludo
Natasha ta magantu kan shiga jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi magana kan shiga jam'iyyar APC.
A yayin wata hira da aka yi da ita, Sanata Natasha ta ce ba za ta taba komawa APC ba saboda wasu dalila nata na karan kanta.
Sanatar ta ce har yanzu akwai wasu daga fadar shugaban kasa da ke ci gaba da yi mata tayin ta dawo jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


