Wike/Fubara: An Fara Samun Hatsaniya game da Nada Kwamishinoni a Rivers

Wike/Fubara: An Fara Samun Hatsaniya game da Nada Kwamishinoni a Rivers

  • Sabuwar rigima na kunno kai tsakanin bangaren Gwamna Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Rigimar na da alaka ne da batun rabon mukaman kwamishinoni a Rivers bayan dawowar mulkin dimukradiyya
  • Duk da sulhun da Shugaba Bola Tinubu ya yi, har yanzu ba a magance matsalolin siyasar Rivers ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Wata sabuwar takaddama na kunno kai tsakanin bangaren Gwamna Siminalayi Fubara, da na Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Rigimar ta kunno kai ne kan wasu muhimman bangarori na yarjejeniyar sulhu da Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani ya cimma watanni da suka gabata.

Tsugune ba ta kare ba tsakanin Fubara da Wike
Nyesom Wike da Gwamna Sim Fubara. Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Punch ta ce bangarorin biyu suna rigimar ce kan rashin jituwa game da kujerun kwamishinoni a jihar da ake shirin nadawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na da nasaba da yadda za a tsara sabuwar majalisar zartarwar jihar, musamman jerin sunayen kwamishinoni.

Kara karanta wannan

Wasu manya a Kano sun ajiye Abba a gefe, sun ce Barau suke so a 2027

Yadda aka sulhunta Wike da Fubara

Za a tuna cewa bayan rikicin siyasa mai tsanani da ya kai ga ayyana dokar ta-baci na tsawon watanni shida a Rivers, Shugaba Tinubu ya shiga tsakani a watan Yunin 2025.

Zaman sulhun ya hada Wike da Fubara a wani taron sirri a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Bayan taron, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an cimma sulhu.

A wancan lokaci, Wike ya ce babu sauran gaba tsakanin su, yayin da Fubara ya ce dole ne a kare yarjejeniyar domin ci gaban jihar.

Har yanzu ana fama da rikicin siyasa

Sai dai bincike ya nuna cewa bayan watanni da cimma sulhun, rikicin siyasar bai lafa ba, domin manyan batutuwan da suka haddasa shi har yanzu suna nan daram.

Bayan dawo da Majalisar Dokokin Jihar Rivers aiki, Kakakin Majalisar, Martin Amaewhule, ya bukaci gwamna ya mika sabon jerin sunayen kwamishinoni.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume da Oshiomhole sun gwabza a majalisa kan tantance Omokri

Fubara dai ya rike kwamishinoni takwas da hukuncin Kotun Koli bai shafe su ba, bayan ya rushe majalisar zartarwa bayan karewar dokar ta-baci.

Majiyoyi sun ce ’yan majalisar suna shirin kin amincewa da duk wani kwamishina da ba ya goyon bayan bangaren Wike, domin ci gaba da rike tasiri a siyasar jihar.

Ana zargin Wike da neman iko a Rivers
Ministan Abuja a Najeriya, Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: UGC

Zargin da ake yi wa Wike

Wani babban jigo a jam’iyyar PDP ya zargi Wike da neman kusan kwamishinoni 12, abin da ya ce ya yi yawa.

Sai dai wani abokin siyasar Wike, Chimelem Wodi, ya musanta wannan zargi, yana cewa tsohon gwamnan ba ya buƙatar irin wannan iko.

Ya ce an riga an warwaren rikicin tun bayan shiga tsakani da Shugaba Tinubu ya yi a wancan lokaci, cewar TheCable.

'Ina tare da Tinubu' - Nyesom Wike

An ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Wike ya nuna cewa bai taba nadama ba kan goyon bayan da ya nunawa Shugaba Bola Tinubu tun daga shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Jami'in kwastam da ya yi fatali da cin hancin $50,000 ya samu karin girma

Ministan ya bayyana daliin da ya sa ya zabi ya goyi bayan Tinubu duk da a wancan lokacin yana cikin jagororin 'yan adawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.