Jam'iyyar APC Ta Cimma Matsaya, Ta Tsaida 'Dan Takarar Gwamnan Osun a Zaben 2026

Jam'iyyar APC Ta Cimma Matsaya, Ta Tsaida 'Dan Takarar Gwamnan Osun a Zaben 2026

  • Jam'iyyar APC ta zabi tsohon shugaban NIWA ta kasa, Bola Oyebamiji a matsayin dan takararta na gwamna a zaben jihar Osun na 2026
  • Wakilan APC daga kananan hukumomi 30 na jihar Osun ne suka tabbatar da Oyabamiji bayan kada kuri'ar murya a zaben fitar da gwani
  • Gwamna Monday Okpebholo na jihar Osun, wanda shi ne shugaban kwamitin zaben, ya tabbatar da nasarar Oyebamiji a hukumance

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsaida dan takarar gwamna a zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar a shekarar 2026.

APC ta cimma yarjejeniyar masalaha tsakanin masu neman tikitin takarar gwamna a Osun bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sa baki a kwanakin baya.

Oyebamiji.
Tsohon shugaban hukumar NIWA ta kasa, Bola Oyebamiji ya zama dan takarar gwamnan APC a Osun Hoto: @ImranMuhdz
Source: Twitter

Oyabamiji ya zama dan takarar APC a Osun

Kara karanta wannan

Jita jita ta ƙare: Mataimakin gwamna da aka garzaya da shi asibiti ya mutu

Jaridar Punch ta tattaro cewa tsohon shugaban Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa na Cikin Gida ta Ƙasa (NIWA), Bola Oyebamiji, ne ya samu nasarar zama dan takarar APC a Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyebamiji ya samu nasarar zama dan takara bisa yarjejeniyar hadin kai da aka cimma a taron zaben fitar da gwani da APC ta shirya yau Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025.

Nasarar Oyebamiji ta biyo bayan wani ƙuduri da wasu ’yan takarar gwamna biyu, Kunle Adegoke (SAN) da Sanata Babajide Omoworare, suka gabatar a wajen zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar.

An gudanar da zaben fitar da gwanin jam'iyyar APC ne a harabar makarantar Ebunoluwa Group of Schools da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun

APC ta tabbatar da nasarar Oyebamiji

Shugaban kwamitin zaɓen na APC kuma Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya miƙa ƙudurin ga kaɗa ƙuri’a ta murya, inda ya samu cikakken goyon bayan mambobin jam’iyyar da suka halarci wurin.

Daga bisani, Okpebholo ya bayyana cewa:

"Bisa ikon da aka ba ni, ina gabatar muku da Bola Oyebamiji a matsayin ɗan takarar gwamnan Osun na jam’iyyarmu ta APC.”

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, Gwamna Fubara ya yi wa Tinubu alkawari kan zaben 2027

Tun farko, rahotanni sun nuna cewa an fara zaben fitar da gwanin ne da isowar shugaban kwamitin, Gwamna Monday Okpebholo, wanda ya bayyana cewa ɗan takarar zai fito ne ta hanyar tabbatarwa da amincewar kowa.

Ya isa wajen taron ne tare da mataimakin shugaban kwamitin, Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da sauran mambobin kwamitin zaɓen, ciki har da Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.

Gwamna Monday Okpebholo.
Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo a wurin taro Hoto: Monday Okpebholo
Source: Twitter

Sauran mambobin kwamitin da APC ta kafa sun hada da Dakta Obafemi Hamzat wanda ya wakilci Gwamnan Jihar Lagos, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.

Daily Trust ta ce Jimillar wakilai 1,660 da aka zabo daga kananan hukumomi 30 da kuma mazabu 332 a jihar Osun sun tabbatar da Oyebamiji, wanda aka amince da shi a matsayin dan takarar masalaha.

Gwamna Adeleke ya lashe tikitin Accord

A baya, kun ji cewa jam'iyyar Accord ta bayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani da aka gudanar a Osogbo.

Gwamna Adeleke, wanda shi kaɗai ne ya tsaya takara a zaben fitar da gwanin, ya samu nasara da da kuri’u 145 daga cikin 150 da wakilan jam'iyyar suka kada.

Kara karanta wannan

Zaben 2026: Gwamna Adeleke ya samu tikitin takara bayan ya fice daga jam'iyyar PDP

Shugaban jam’iyyar Accord na ƙasa, Maxwell Mgbudem, ya mika wa Adeleke takardar shaidar lashe zaben, tare da taya shi murna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262