‘Ko $1bn Aka Ba Ni, ba Zan Shiga Sabgar ba’: Malamin Addini Ya Tsinewa Siyasa
- Fitaccen Fasto a Najeriya, David Oyedepo ya jaddada aniyarsa ta kin jinin shiga siyasa saboda ba abin da ya shirya ba kenan
- Malamin addinin Kirista ya ce ko biliyoyin kudi aka ba shi ya tsoma kansa cikin harkokin siyasa ba zai taba amincewa ba
- Shugaban cocin 'Living Faith' ya bukaci mabiya su mayar da hankali kan kiran Allah, domin su jagoranci duniya ta wannan zamani
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Cocin Living Faith Church Worldwide (LFC), Fasto David Olaniyi Oyedepo, ya sake jaddada matsayinsa kan shiga siyasa.
Faston ya ce ba wani abu da zai ja hankalinsa ya shiga siyasar jam’iyya, ko da kuwa an ba shi dala biliyan ɗaya.

Source: Twitter
Fasto ya caccaki yadda ake siyasa
Fasto Oyedepo ya bayyana hakan ne yayin taron bikin shekara-shekara na cocin, Shiloh 2025, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce shiga siyasa ya sabawa tsarin rayuwarsa da manufar da Allah ya dora masa wanda zai bi har karshen rayuwarsa.
A yayin jawabin nasa, ya bukaci mabiya cocin da su mai da hankali kan fannin da Allah ya kira su, inda za su iya mulkar duniyarsu da kuma kasancewa cikin rundunar Allah ta ƙarshe.
A cewarsa, ya taba gargadin coci tun a shekarar 2015 cewa wani mawuyacin lokaci na tafe, kuma abubuwan da suka faru daga baya sun tabbatar da gargadin.
Ya ce matsaloli sun mamaye duniya, amma mafita ba ta fito daga siyasar jam’iyya kai tsaye ba.
Oyedepo ya ce:
“Siyasar jam’iyya ba ta cikin kirana. Ko an ba ni dala biliyan ɗaya domin in shiga siyasa, ba zan amince ba, domin hakan ya kauce wa tafarkin da Allah ya sanya ni.”

Source: Twitter
Albashir da Fasto ya yi ga yan kasa
Faston ya kara da cewa duniya na cikin duhu mai tsanani, amma kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna a Romawa 8:19, duniya na jiran bayyanar bayin Allah.
Ya jaddada cewa rundunar Allah na gab da fitowa fili domin bayar da mafita ga matsalolin ƙasa, ta hanyar tsari irin na Annabi Yusuf da Annabi Daniyel.
A cewarsa, wannan lokaci ne na abubuwan al’ajabi da idanun mutane ba su taba gani ba, kuma kunnuwa ba su taba ji ba.
A karshe, Oyedepo ya bukaci mabiya cocin da su tsaya tsayin daka a imaninsu, su mai da hankali kan kiran da Allah ya ba su.
Ya bukaci su yi aiki domin canza al’umma ta hanyar gaskiya, adalci da tsoron Allah, ba wai ta hanyar neman madafun iko na siyasa ba.
Kano: Malami ya shiga siyasa bayan komawa APC
A baya, an ji cewa Sanata Barau Jibrin ya karɓi shugabannin addini, ‘yan siyasa da matasa daga NNPP a Kano, waɗanda suka sauya sheka zuwa APC.
Jagoran Qadiriyya Riyadul Jannah a Getso, Malam Abubakar Mai Kanzu ya goranci daruruwan mabiyansa zuwa jam'iyyar APC.
Shi kuma Alhaji Ade ya yaba da kafa cibiyoyin NOUN a Kano ta Arewa, da ginin makarantar NSCDC da filin wasa domin ci gaban matasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

