Wike Ya Sake Tabo Batun Goyon Bayansa ga Tinubu a Zaben 2023

Wike Ya Sake Tabo Batun Goyon Bayansa ga Tinubu a Zaben 2023

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake jaddada goyon bayansa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Wike ya nuna cewa bai taba nadama ba kan goyon bayan da ya nunawa Shugaba Bola Tinubu tun daga shekarar 2022
  • Ministan ya bayyana daliin da ya sa ya zabi ya goyi bayan Tinubu duk da a wancan lokacin yana cikin jagororin 'yan adawa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake tsokaci kan goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Nyesom Wike ya ce bai da wata nadama game da goyon bayan da ya ba Shugaba Tinubu tun daga shekarar 2022.

Wike ya ce bai yi nadamar goyon bayan Tinubu ba
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Lere Olayinka, ya fitar a ranar Asabar, 13 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

'Ko $1bn aka ba ni, ba zan shiga sabgar ba': Malamin addini ya tsinewa siyasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nyesom Wike ya bayyana hakan ne yayin wani biki na musamman da aka shirya domin cika shekaru 58 da haihuwarsa.

Me Wike ya ce kan goyon bayan Tinubu?

Ministan ya jaddada cewa matsayarsa ba ta taɓa sauyawa ba kafin, lokacin, da kuma bayan zaɓen shugaban kasa na 2023.

Wike ya ce dukkan matakan siyasar da yake ɗauka suna dogara ne kan mutunci da nagarta, yana mai kara cewa bai taɓa ɓoye goyon bayansa ga Shugaba Tinubu ba tun daga farko.

Ya tuna cewa a lokacin shirin tunkarar zaɓen 2023, shi ne kaɗai daga cikin manyan jagororin babbar jam’iyyar adawa da ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu.

Wike ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne bisa adalci, daidaito da gaskiya, tare da kudurinsa na cewa ya dace mulki ya koma Kudancin Najeriya.

Wike ya sha yabo daga manyan mutane

A bikin da aka gudanar gidansa da ke Abuja, shugabanni daga bangarorin siyasa daban-daban sun hallara domin taya tsohon gwamnan na jihar Rivers murnar nasarori da tasirinsa a siyasa, jaridar The Guardian ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

'Duk da ba jam'iyya daya muke ba': Tinubu ya yaba jajircewar Wike a gwamnatinsa

Daga cikin mahalarta taron akwai ’yan majalisar tarayya daga jihar Rivers, na yanzu da na baya, ’yan majalisar dokokin jihar Rivers karkashin jagorancin, Martins Amaewhule, shugabannin kananan hukumomi, da kuma abokai da abokan hulɗar siyasa na kusa da shi.

Masu jawabi sun jinjina wa ministan, suna bayyana shi a matsayin mutum mai nasara kuma jajirtaccen ɗan siyasa, wanda tasirinsa ya bayyana a sassan kasar, suna kuma ƙarfafa masa gwiwa da tabbatar masa da ci gaba da goyon bayansu.

Martins Amaewhule, wanda ya jagoranci ’yan majalisa 27 zuwa gidan Wike, ya gode wa ministan bisa kasancewarsa shugaba mai karfin gwiwa da kowa ke jingina da shi.

Ya yi alkawarin ci gaba da biyayya da goyon bayan majalisar gare shi, yana cewa:

“Duk inda jagoranmu (Wike) ya dosa, za mu bi shi, duk wanda yake goyon baya, mu ma za mu goya masa baya."
Wike zai ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu
Nyesom Wike tare da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @GovWike
Source: Twitter

Ministan Abuja ya yi godiya

A nasa martanin, ministan ya godewa abokansa na siyasa da abokan aikinsa, yana mai yabawa rawar da suka taka wajen gina tafiyarsa ta shugabanci.

Ya ce yana samun gamsuwa wajen aiki tare da mutanensa, kuma ya yi alkawarin ci gaba da haɗa kai da su domin amfanin al’ummar Jihar Rivers da Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya goyi bayan wa'adi 1 a mulki, ya fadi amfaninsa

Wike, wanda ya ce suka da cin mutunci na daga cikin abubuwan da ke kara masa ƙwarin gwiwa, ya bayyana cewa ba ya damuwa da masu suka ko zagi.

An kammala taron ne da addu’o’i na musamman ga ministan da iyalansa.

Wike ya soki gwamnonin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ragargaji wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP.

Nyesom Wike ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed da Gwamna Seyi Makinde, sun yi kadan su kore shi daga PDP.

Ministan ya nuna cewa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Gwamna Seyi Makinde na Oyo sun shiga PDP lokacin da ya riga ya dade a cikinta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng