Ta Tabbata, Gwamna Ya Fara Laluben Jam'iyyar da Zai Koma idan Ya Fice daga PDP
- Hadimin gwamnan jihar Filato, Hon. Istifanus Mwansat ya musanta rahoton da ake jingina masa cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya koma APC
- Ya tabbatar da cewa Gwamna Mutfwang ya fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin duba yiwuwar ficewa daga PDP zuwa wata jam'iyyar
- Rahoto ya nuna cewa jita-jitar sauya shekar Gwamna Mutfwang ta haddasa ce-ce-ku-ce da musayar yawu a tsakanin magoya bayan PDP da APC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Gwamnatin Filato ta tabbatar da cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin duba yiwuwar ficewa daga PDP.
Mai ba gwamnan Filato shawara kan harkokin siyasa, Hon. Istifanus Mwansat, ya bayyana cewa mai gidansa bai sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ba tukuna.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa hadimin gwamnan ya fadi haka ne yayin da yake martani kan wani rahoto da aka danganta da shi da ke cewa Gwamna Mutfwang ya koma APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da gaske Gwamna Mutfwang ya koma APC?
A wata tattaunawa da aka yi da shi jiya Alhamis, Istifanus ya ce har yanzu gwamnan na duba zabin da yake da shi, amma bai kai ga yanke hukunci kan jam'iyyar da zai koma ba.
Ya tabbatar da cewa Gwamna Mutfwang na ci gaba da tattaunawa da neman shawarwari daga manyan jagororin jam’iyyar PDP kafin ya yanke hukunci.
Jita-jitar sauya shekar gwamnan ta haddasa ce-ce-ku-ce tsakanin mambobin PDP da APC a Filato, inda magoya bayan Mutfwang da na shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, suka fara musayar kalamai.
Gwamnan Filato na iya barin PDP
Da yake martani kan rahoton, Hon. Istifanus ya karyata cewa Mutfwang ya riga ya sauya sheka, yana mai cewa gwamnan har yanzu yana cikin PDP.
"An fara tattaunawa amma hakan na yana nufin ya riga ya sauya sheka ba ne, Wannan wani zaɓi ne kawai da ke teburin tattaunawa. A halin yanzu bai koma APC ba. Yana shawara da manyan ‘yan siyasa a matakai daban-daban.”
“Idan ka ce ya sauya sheka, hakan na nufin komai ya kammala, ya yi rajista da APC kuma ya yi murabus daga PDP. Wannan bai faru ba, babu inda na ce Mutfwang ya sauya sheka,” in ji shi.

Source: Twitter
A ranar Lahadi da ta gabata, shugaban APC na jihar Filato, Hon. Rufus Bature, ya ce jam’iyyar ba ta samu wata sanarwa ko tuntuba game da yuwuwar shigowar gwamnan ba.
Ya kuma jaddada cewa dole a bi matakan da suka dace kafin kowa ya iya shiga jam’iyyar, kamar yadda Vanguarda ta ruwaito.
An roki gwamnan Filato ya koma APC
A wani labarin, kun ji cewa wata kungiyar magoya bayan PDP a jihar Filato ta ce akwai bukatar Gwamna Caleb Mutfwang ya hada inuwa daya da Bola Tinubu a siyasa.
Kungiyar ta bukaci Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, da ya koma jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya cikin gaggawa.
Bisa haka, kungiyar ta rubuta wasika ta musamman kuma ta kai wa gwamnan har gidan gwammati da ke Jos, babban birnin jihar Filato.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

