"Ina Kaunar Jam'iyyar": Gwamna Adeleke Ya Fadi Aininin Dalilin Ficewa daga PDP
- Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tabbatar da komawa jam'iyyar AP bayan ya fice daga PDP mai adawa a Najeriya
- Ademola Adeleke ya tabbatar da cewa yana matukar kaunar PDP, amma dole ya hakura ya fice daga cikinta saboda wasu dalilai
- Gwamna Adeleke yana da kwarin gwiwar cewa mutanen jihar Osun za su sake ba shi kuri'u a zaben shekarar 2026 da ke tafe
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan ficewarsa daga jam'iyyar PDP bayan ya koma AP.
Gwamna Adeleke ya karyata rade-radin cewa ya yi watsi da jam’iyyar PDP, wadda ta ba shi farin jini a siyasa.

Source: Twitter
Gwamna Adeleke ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Tv a ranar Laraba, 10 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan
Zaben 2026: Gwamna Adeleke ya samu tikitin takara bayan ya fice daga jam'iyyar PDP
Gwamna Ademola Adeleke ya koma jam'iyyar AP
A ranar Talata, Adeleke ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar AP a matsayin wadda zai nemi tazarce karkashinta a shekarar 2026.
Gwamna Adeleke ya ce ya shiga AP ne tun ranar 6 ga Nuwamba 2025, domin ya tsaya takara karkashin jam’iyyar a zaben da za a gudanar a watan Agustan shekara mai zuwa.
Meyasa Gwamna Adeleke ya fice daga PDP?
Gwamna Adeleke ya bayyana cewa yana matukar kaunar PDP, amma rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ya tilasta masa neman wuri mai kwanciyar hankali domin sake tsayawa takarar gwamna a 2026.
“Ina son PDP, amma rikice-rikicen da ake ciki sun yi yawa. Na yi bakin kokarina, na yi iya yi na, amma kullum abubuwa sai taɓarɓarewa suke."
"Don haka, a matsayina na mutum mai hangen nesa, sai na tambayi kaina, ‘Ina zan nufa daga nan?’”
“Saboda haka na yanke shawarar zuwa jam’iyyar AP. Ba gaskiya ba ne cewa na yi watsi da PDP. Ina son PDP, amma dole na kare kaina da jihata saboda mu ci gaba da aikin alheri da muke yi a Osun."
- Gwamna Ademola Adeleke

Source: Twitter
Adeleke na fatan samun nasara a zaben gwamna
Gwamnan ya kara da cewa jam’iyya ba ita ce abu mafi muhimmanci ga ’yan Osun ba, saboda mutane sukan zabi mutum bisa aikinsa, ba jam’iyyar da ya fito ba.
“Ina da yakini cewa mutanen Osun suna kaunata. Ba jam’iyya ke magana yanzu ba. Mutanen Osun masu wayo ne, ba jam’iyya ce abu mai muhimmanci a wajensu ba, mutum ne. Me ka yi? Ina da tarihin aiki, kuma shi mutane za su yi la’akari da shi.”
- Gwamna Ademola Adeleke
Gwamna Adeleke ya ce cikin shekaru uku da suka gabata gwamnatinsa ta cimma abubuwa masu yawa, don haka yana da tabbacin cewa za a zabe shi bisa aikinsa, ba bisa tutar jam’iyya kawai ba.
'Dan majalisa ya fice daga PDP zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar wakilai daga jihar Kebbi, Mansur Musa ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC.
Mansur Musa ya bayyana cewa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan ya raba gari da PDP.
Dan majalisar ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka addabi PDP sun taka rawar gani wajen shawarar da ya yanke ta barin jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

