PRP Ta Rufe Kofa da Aka Fara Rade Radin Gwamna Bala Zai Fice daga PDP
- Jam'iyyar PDP mai adawa na ci gaba da rasa manyan jiga-jiganta yayin da ake shirye-shiryen babban zabe mai zuwa a shekarar 2027
- Awanni kadan bayan ficewar gwamnan Ribas, an fara rade-radin Gwamna Bala Mohammed na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PRP
- PRP ta bayyana cewa ko da wannan labari gaskiya ne, ba za ta karbi Gwamna Bala ba saboda yadda ya maida jihar Bauchi baya a mulkinsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - An fara rade-radin cewa shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed na shirye-shiryen sauya sheka zuwa PRP.
Wannan jita-jita ta fara yawo ne sa'o'i kadan bayan Gwamna Siminalayi Fubara na Ribas ya fita daga PDP zuwa APC, sannan Gwamna Ademola Adeleke na Osun ya yanki katin jam'iyyar Accord.

Source: Twitter
PRP ta rufe wa gwamnan Bauchi kofa
Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa jam'iyyar PRP reshen Bauchi ta toshe kofar karbar Gwamna Bala Mohammed, tana mai cewa ba shi da matsuguni a inuwarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PRP ta yi watsi da rade-radin cewa Gwamna Bala Mohammed zai koma jam’iyyar a wata sanarwa da sakatarenta na jihar, Hon. Wada Abdullahi, ya fitar ranar Laraba.
Jam’iyyar PRP ta ce:
"Ko da akwai gaskiya a jita-jitar cewa Gwamna Bala zai koma PRP, muna sanar da jama’a cewa ba mu da wurin da za mu karbe shi a jam’iyyarmu.”
Me yasa PRP ba za ta karbi Gwamnan ba?
PRP ta zargi gwamnan da rashin aiwatar da ayyyuka masu kyau a wa'adin mulkinsa da kuma nuna halayen da ba su dace ba, musamman abin da shi da magoya bayansa suka yi a hedkwatar PDP da ke Abuja.
Har ila yau, jam'iyyar ta soki manufofin Gwamna Bala, tana mai cewa da yawansu sun cutar da Bauchi, ciki har da ƙirƙirar sababbin masarautu da nadin dan uwansa a matsayin Sarki.
PRP ta ce waɗannan abubuwa “za su buƙaci a gudanar bincike da yiwuwar soke su” idan ta kafa gwamnati a 2027.
PRP ta dauki alkawari idan ta karbe Bauchi
Jam’iyyar PRP ta ce idan ta karbi mulkin Bauchi a 2027:
“Za mu gudanar da cikakken bincike kan gwamnatinsa, mu gurfanar da duk wanda aka samu da laifi, kuma mu sake duba manufofin da suka kawo cikas ga ci gaban Bauchi.”
Sai dai jam’iyyar ta ce ta buɗe ƙofofinta ga duk wanda ya bada gudunmawa ga cigaban Bauchi kuma zai taimaka wa jam’iyyar ta ci gaba.
PRP ta ƙara da cewa burinta shi ne ta tsaya a kan gaskiya, tsabta, da hidima ga al’umma, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Source: Twitter
Gwamna Fubara ya bar PDP zuwa APC
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya sanar da sauya shekarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki a kasar nan.
Hakan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Gwamna Fubara ya ziyarci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadar gwamnatin tarayya, Abuja.
Gwamnan ya ce duka magoya bayansa sun amince da wannan shawara da ya yanke ta komawa APC saboda a cewarsu, hakan zai ba su damar marawa Tinubu baya a 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


