Dan Majalisa Ya Gaji da Rikicin PDP, Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake rasa daya daga cikin 'yan majalisar wakilan da take da su
- Dan majalisar wakilai daga jihar Kebbi, Mansur Musa, ya sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
- Mansur Musa ya bayyana cewa rikice-rikicen da suka addabi PDP, na daga cikin dalilan da suka sanya ya raba gari da jam'iyyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar Aliero/Gwandu/Jega a jihar Kebbi, Mansur Musa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
Mansur Musa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan ya raba gari da PDP.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa an bayyana wannan sauyi nasa ne a zauren majalisar wakilai a ranar Talata, 9 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta takardar sauya shekarsa a gaban ‘yan majalisa.
Dan majalisar PDP ya koma APC
A cikin bayaninsa, Mansur Musa ya ce PDP ta tsinci kanta cikin tsananin rikice-rikice, sabani marasa iyaka da matsalolin da ba a warware ba, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
Ya ce rikice-rikicen sun gurgunta jam’iyyar har ta kasa zama wani dandali wanda yake da kwararan manufofi.
“A watannin baya-bayan nan, PDP ta ruguje saboda tsananin rarrabuwar kai, rikice-rikice da matsalolin da ba a magance ba, wadanda suka lalata hadin kai, suka raunana tsaftar tafiyar jam’iyya, suka kuma hana ta bayar da jagorancin da ya dace.”
- Mansur Musa
Mansur Musa ya ce irin wadannan matsaloli sun haifar da yanayin da bai dace da aikin da al’ummar mazabarsa suka ba shi ba.
“Wadannan sabani sun haifar da yanayi wanda bai dace da amanar da al’ummata suka dora min ba."
- Mansur Musa
Ya yi tunani kafin ficewa daga PDP
Ya kara da cewa wannan mataki nasa ya biyo bayan dogon tunani da shawarwarin da ya yi da shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki a mazabarsa.
“Bayan dogon tunani da kuma tattaunawa da al’ummata, shugabannin gargajiya da ’yan siyasa, a bayyane yake cewa ci gaba da zama cikin jam’iyyar da ke fama da rikicin da bai karewa zai cutar da nagartaccen wakilci da aka dora mini.”
- Mansur Musa
Meyasa Mansur Musa zai koma APC?
Hakazalika ya ce APC na da tsari mai karfi da cika alkawura, wanda ya dace da burin mazabarsa.
“APC na da tsari mai kwari, tare da daidaito da buri da bukatun mazabata, kuma tana da kwanciyar hankali da ake bukata don gudanar da aiki yadda ya kamata.”
- Mansur Musa

Source: Facebook
Bayan karanta takardar, ’yan majalisa daga APC da shugabanninta sun yi masa tarba cikin farin ciki.
Wannan sauyi da Mansur Musa ya yi ya kara yawan jerin ’yan siyasan PDP da ke barin jam’iyyar, saboda rikicin cikin gida da rarrabuwar kawuna, ciki har da bangarorin da suke goyon bayan Nyesom Wike da Tanimu Turaki.
Gwamnan Taraba zai koma APC daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, zai sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Gwamna Agbu Kefas zai shiga jam'iyyar a watan Janairu, 2026 kamar yadda shugaban APC na Taraba, Ibrahim Tukur ya tabbatar.
Shugaban na APC ya jaddada cewa gwamnan jihar na Taraba ya cika dukkanin ka'idojin da ake bukata na zama mamban jam'iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


