Ganduje Ya Hango Matsalar da APC za Ta Iya Shiga a Kano kan Ayyana Dan Takara
- Abdullahi Umar Ganduje ya ce lokaci bai yi ba domin ayyana wani a matsayin ɗan takarar gwamna na APC a 2027 a jihar Kano
- Tsohon shugaban APC na kasa ya gargadi magoya baya kan cewa gaggawar ayyana 'yan takara na iya raba kan jam’iyya a jihar
- Rikicin siyasa ya fara tashi ne bayan wasu manyan ‘yan jam’iyya sun fara tallata Sanata Barau Jibrin a matsayin dan takara a 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar APC a jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya gargadi mambobin jam’iyyar da su daina gaggawar talla ko ayyana wanda suke son ya tsaya takarar gwamna a zaben 2027.
Wannan gargadi nasa ya biyo bayan yadda wasu kusoshin jam’iyyar suka fito fili suka ce Sanata Barau Jibrin ne za su mara wa baya a takarar.

Source: Twitter
A hira da BBC Hausa, Ganduje ya ce irin wannan gaggawa na iya haifar da rikici da rabuwar kai, musamman ma a wannan lokaci da jam’iyyar ke ƙoƙarin ƙarfafa hadin kanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin waɗanda suka janye kalamansu akwai Baffa Takai, wanda ya nemi afuwa daga mambobin jam’iyyar saboda rawar da ya taka wajen tayar da batun tun da wuri.
Ganduje ya gargadi 'yan APC a jihar Kano
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Ganduje ya ce bai kamata a fara faɗin cewa wannan ya fi wancan ba, domin irin wannan hali na janyo matsaloli cikin jam’iyya.
Ganduje ya yi gargadi da cewa ya kamata mutane su daina tallata ‘yan takara da sunan cewa wannan yafi wannan domin wannan halin zai kawo rabuwar kawuna.
Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta kai ga lokacin da za ta buɗe kofar zaɓen ‘yan takara, kuma idan lokacin ya yi, wadanda suka cancanta za su fito.
Bayani game da taron APC a Kano
Rahotanni sun nuna cewa a wani taron masu ruwa da tsaki da APC ta yi a Kano, mahalarta sun bayyana cewa su na jiran umarnin Dr Abdullahi Umar Ganduje domin ya fayyace hanyar da jam’iyyar za ta bi.
Sai dai duk da haka, har yanzu akwai masu fitowa suna ayyana wanda suke so ya tsaya takarar gwamna, abin da ke nuna cewa ba a gama shawo kan lamarin ba.

Source: Facebook
Wasu jiga-jigan jam’iyyar sun nuna fargabarsu cewa idan ba a yi taka-tsantsan ba, gaggawar ayyana gwanaye ka iya lalata daidaituwar jam’iyyar kafin babban zaɓen 2027.
Masu sharhi na ganin cewa irin wannan gargadin na Ganduje na iya zama wani mataki na kare martabar jam’iyya da tabbatar da cewa ba a sake maimaita matsalolin rabuwar kai da jam’iyyar ta fuskanta a wasu jihohi ba.
APC ta gargadi minista kan tallata Barau
A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar APC ta gargadi ministan Najeriya, Yusuf Ata kan ayyana dan takarar 2027 a Kano.
Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa ministan ba shi da hurumin ayyana dan takara a jam'iyyar.
Lamarin ya biyo bayan ayyana Sanata Barau Jibrin a matsayin dan takara da Ata ya yi yana cewa ya kamata a goya masa baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


