"Sun Yi Kadan": Wike Ya Ware Gwamnoni 2 Ya Yi Musu Saukale kan Rikicin PDP
- Jam'iyyar PDP na ci gaba da fama da rikicin cikin gida da ya dade yana addabarta, wanda hakan ya sanya ta dare gida biyu
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya cika baki da cewa babu wanda ya isa ya kore shi daga jam'iyyar PDP
- Wike ya bayyana cewa ya dade a cikin PDP kuma wadanda ke kokarin raba shi da ita sun yi kadan domin ba zai yarda da hakan ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba a isa a kore shi daga jam'iyyar PDP ba.
Wike ya bayyana cewa ba za a kore shi daga PDP ba, musamman ma daga mutanen da suka shiga jam’iyyar bayan shi.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce Wike ya yi wannan jawabin ne a ranar Lahadi yayin wani zaman NEC na ɓangaren jam’iyyar PDP da yake jagoranta, wanda aka gudanar a gidansa da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Gwamna Seyi Makinde na Oyo sun shiga PDP lokacin da ya riga ya dade a cikinta.
Jam'iyyar PDP na fama da rikice-rikice
A watan da ya gabata, ɓangaren PDP da Makinde da Bala ke mara wa baya ya kori Wike da magoya bayansa, ciki har da tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon sakatare jam'iyyar na kasa Samuel Anyanwu.
Sauran sun hada da tsohon sakataren tsare-tsare, Umar Bature, tsohon lauyan jam'iyya, Kamaldeen Ajibade da wasu shugabanni daga jihohi daban-daban.
Tun daga lokacin, ɓangaren Wike ya kafa sabon kwamitin gudanarwa na kasa (NWC), BoT da NEC.
Nyesom Wike ya dauki zafi kan rikicin PDP
Wike ya bayyana cewa ya kasance cikin PDP tun daga lokacin da aka fara shirin kafa ta a shekarar 1990, inda ya kara da cewa babu wanda ya isa ya kori mutanen da suka yi wa jam'iyyar hidima, za a samu rahoton a jaridar Vanguard.
“Ta yaya mutanen da suka same ni a gidana za su kore ni? Ba zan taba bari hakan ta faru ba."
“Ku tambayi Bala Mohammed wace jam'iyya ya yi takarar sanata. Jam'iyyar mu ta ba mutane da dama mafaka inda suka zama sanatoci da gwamnoni."
“Amma yanzu suna tunanin za su iya korar mutanen da suka yi sadaukarwa ga jam'iyyar tun kafuwarta. Idan an bar su sun yi hakan a baya, mu ba za mu kyale su ba."
- Nyesom Wike

Source: Facebook
Wike ya caccaki gwamnonin PDP
Wike ya caccaki bangaren Kabiru Tanimu Turaki wanda Gwamna Bala da Seyi Makinde ke marawa baya, kan bin umarnin kotu tare da gudanar da haramtaccen babban taro.
"Kun yi babban taro ba tare da bin umarnin kotu ba, yanzu kuma kuna neman babbar kotun tarayya ta amince da ku. Idan har INEC ta amince da ku, me yasa kuka sake komawa kotu."
- Nyesom Wike
Ministan ya yi gargadin cewa hakan zai iya gurbata PDP, inda ya nuna cewa dole ne shugabanni su tashi tsaye domin kare jam'iyyar wadda aka kafa a shekarar 1998.
Wike ya kori shugaban hukumar FCT-IRS
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi garambawul a hukumar tattara harajin FCT watau (FCT-IRS).
Nyesom Wike ya tsige shugaban rikon kwarya na hukumar tattara Haraji ta FCT (FCT-IRS), Michael Ango, daga mukaminsa nan take.
Ministan na Abuja ya umarci jami’i mafi girma a FCT-IRS da ya gaggauta karɓar jagoranci domin ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


