Gwamna Agbu Kefas ba Zai Shiga Jam'iyyar APC a 2025 ba, An Sanya Sabon Lokaci
- Za a gudanar da gagagrumin bikin sauya shekar Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba zuwa jam'iyyar APC a watan Janairu, 2026
- Shugaban APC na Taraba, Ibrahim Tukur, ya ce jam'iyyar ta ga dacewar sauya lokacin taron zuwa Janairu saboda bukukuwan Disamba
- Ibrahim Tukur ya kuma sanar da cewa APC ta dakatar da wasu shugabanni a matakin gunduma saboda karya dokokin gudanarwar jam'iyyar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Taraba - Shugaban jam'iyyar APC na jihar Taraba, Ibrahim Tukur, ya tabbatar da cewa Gwamna Agbu Kefas zai shiga jam'iyyar a watan Janairu, 2026.
A kwanakin baya ne Gwamna Kefas ya soke taron shigarsa jam'iyyar APC da aka shirya yi a ranr 19 ga Nuwamba saboda sace dalibai a jihar Kebbi, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.

Source: Twitter
An sauya lokacin shigar gwamna APC
A lokacin, gwamnan jihar na Taraba ya ce zai zama rashin tunani a ce ya aiwatar da wannan taron siyasar alhalin kasar na fama da matsalar tsaro, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Jalingo, babban birnin Taraba a ranar Lahadi, Tukur ya ce gwamnan ya riga da ya yi rajista a gundumarsa.
Tukur ya ce yanzu abin da ya rage shi ne a shirya kwarya-kwaryan taron da zai tabbatar da sauya shekarsa zuwa APC a watan da za mu shiga.
"Akwai tarin ayyuka da shagulgula a Disamba, watan a rikice yake. Ba ma son gayyato mutane daga jihohi alhalin suna shirye-shiryen bikin Kirsimeti da sabuwar shekara da iyalansu."
- Ibrahim Tukur.
Gwamna Kefas zai shiga APC a 2026
Shugaban na APC ya jaddada cewa gwamnan jihar na Taraba ya cika dukkanin ka'idojin da ake bukata na zama mamban jam'iyyar.
Ya bayyana cewa:
"Gwamnan ya aika takarda ga shugabannin gundumarsa, kuma sun karbe shi. A abin da muka tabbatar daga kundin jam'iyya shi ne, Gwamna Kefas yanzu cikakken dan APC ne."
Ya kuma bayyana cewa wasu 'yan majalisar dokokin jihar Taraba 15, da dukkanin mukarraban gwamnatin jihar, sun shiga APC mai mulki a kasa.
"Abin da kuke gani a yanzu shi ake kira kudurar ubangiji. Duk wasu na hannun damar gwamnan sun shiga APC, kuma wasu ma na hanyar shiga. Lallai, babu wani sauran zulumi garemu yanzu."
- Ibrahim Tukur.
Shugaban jam'iyyar ya kuma bayyana cewa shugabannin APC sun amince cewa watan Janairu, 2026 ne ya fi dacewa a gudanar da taron karbar gwamnan.

Source: Twitter
An dakatar da wasu shugabannin APC
Ibrahim Tukur ya kuma sanar da cewa APC ta dakatar da wasu shugabannin jam'iyyar a matakin gundumomi saboda karya dokokin gudanarwar jam'iyyar, in ji rahoton Channels TV.
Shugaban jam'iyyar, a madadin kwamitin SWC na APC ya janye dakatarwar da ya yi wa 'dan majalisar dokokin Taraba, Abel Peter na mazabar Mbamga.
Ya kuma yi martani ga kalaman Atiku Abubakar na cewa zai kwace jihar Taraba, yana mai cewa tuni APC ta kafa iko a gidan gwamnatin Taraba, kuma ba ta da shirin fita.
Gwamna Kefas ya gana da Shugaba Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Agbu Kefas ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya halarci wannan zama, wanda ake ganin yana da alaka da batun taron karbar gwamnan na Taraba.
Wannan dai na zuwa ne bayan Gwamna Kefas da magoya bayansa sun bar PDP zuwa APC amma har yanzu ba a karbe su zuwa jam'iyyar a hukumance ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


