'Dalilin da Ya Sa Atiku Abubakar Ya Ziyarci Goodluck Jonathan'

'Dalilin da Ya Sa Atiku Abubakar Ya Ziyarci Goodluck Jonathan'

  • An yi ta rade-radi da 'yan kunji-kunji bayan Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ziyarci Goodluck Jonathan ne gidansa da ke Abuja kwanaki bayan ya dawo daga kasar Guinea-Bissau
  • Hadimin tsohon shugaban kasar Paul Ibe, ya bayyana dalilin da ya sa Atiku Abubakar ya ziyarci Jonathan bayan an fara yada cewa ziyarar na da alaka da siyasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gana da Goodluck Jonathan a karshen mako.

Atiku ya gana da tsohon shugaban kasar ne bayan ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke Abuja.

Atiku Abubakar ya gana da Goodluck Jonathan
Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku Abubakar ya wallafa hotunan ganawarsa da tsohon shugaban kasar a shafinsa na X da yammacin ranar Lahadi, 7 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Shekaru 15 ana abu 1: Olusegun Obasanjo ya fadi hanyar kawar da Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya bayyana cewa ya ji dadin sake haduwa da tsohon shugaban kasar na Najeriya.

Ziyarar ta janyo cece-kuce a cikin ‘yan siyasa saboda babu cikakken bayani game da abinda suka tattauna.

Meyasa Atiku ya gana da Jonathan?

Sai dai Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ziyarar ba ta da alakar siyasa.

Ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya ziyarci Jonathan ne domin duba lafiyarsa bayan halin tashin hankali da ya shiga a Guinea-Bissau yayin juyin mulkin da aka yi bayan zaben shugaban kasar.

"Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ziyarci tsohon Shugaba Jonathan ne saboda abin da ya faru a Guinea-Bissau."
"Tun daga lokacin ba su hadu ba, ya ga ya dace ya je ya duba shi. Babu wani abu na siyasa a cikin wannan ganawa.”

- Paul Ibe

Hakazalika, mai magana da yawun Goodluck Jonathan, Ikechukwu Eze, ya bayyana cewa bai san abin da suka tattauna ba.

Kara karanta wannan

Me ake kullawa: Atiku ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Jonathan ya gana da Atiku Abubakar
Goodluck Jonathan tare da Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Jonathan ya je Guinea-Bissau

A ranar 26 ga Nuwamba, Jonathan na cikin tawagar shugabannin Afirka da suka makale a Guinea-Bissau bayan yunkurin juyin mulki a kasar.

Ya kasance cikin tawagar haɗin gwiwa ta Tarayyar Afirka (AU), ECOWAS da West African Elders Forum (WAEF) da aka tura domin sa ido kan zaben shugaban kasar.

Karanta wasu karin labaran kan Atiku

Atiku ya gana shugabannin ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya gana da shugabannin jam'iyyar ADC na jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Shugabannin ADC sun ziyarci tsohon dan takarar shugaban kasar na PDP a zabe 2023 ne bisa jagorancin shugaban jam'iyyar na Kogi, Ogga Kingsley.

Kara karanta wannan

IBB ya gano matsalar Arewa, ya fadi dalilin rashin tsaro, talauci a yankin

Ogga Kingsley ya bayyana cewa shugabannin ADC na jihohi suna farin cikin karɓar shi a jam’iyyar, musamman ganin rawar da yake takawa a siyasar Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng