Magana Ta Fito: Dalilin APC Na Kin Karbar Gwamna Mutfwang zuwa Cikinta

Magana Ta Fito: Dalilin APC Na Kin Karbar Gwamna Mutfwang zuwa Cikinta

  • Wasu masana kan harkokin siyasa na ganin cewa gwamnan jihar Plateai, Caleb Mutfwang na son sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Shugaban ADC na jihar Plateau ya yi karin haske kan dalilin da ya sa ba su karbi gwamnan zuwa cikin jam'iyyarsu ba
  • Rufus Bature ya bayyana cewa akwai matakan da dole sai gwamnan ya bi kafin su amince ya zama mamba a jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Shugaban jam’iyyar APC na jihar Plateau, Rufus Bature, ya yi magana kan sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang.

Shugaban na APC ya bayyana dalilin da ya sa ba a karbi Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ba a cikin jam'iyyar.

Ana maganar Mutfwang zai iya komawa APC
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: @CalebMutfwang
Source: Twitter

Rufus Bature ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

'Yan Biyafara sun taru sun harzuka bayan daure Nnamdi Kanu a Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Komawar Mutfwang zuwa APC na jawo cece-kuce

Kungiyoyi daban-daban a jihar sun gudanar da taron manema labarai da gangami, wasu suna goyon bayan shigowar gwamnan APC, yayin da wasu ke adawa da hakan.

Shugabannin APC a jihar, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, sun bayyana kin amincewarsu da shirin gwamnan na komawa APC.

Sai dai Gwamna Mutfwang ya musanta cewa ya sauya sheka, yana mai cewa mambobin APC ne ke matsa masa lamba ya koma jam’iyyar.

Meyasa ba a karbi Mutfwang a APC ba?

Rufus Bature ya ce dole ne gwamnan kamar kowane mai sauya sheka, ya bi tsarin jam’iyya kafin a karɓe shi a hukumance.

Ya kara da cewa dole ne a samu tattaunawa da yarjejeniya kafin jam’iyyar ta amince da karɓar sa.

“Ya kamata Gwamnan ya bi madaidaicin tsari. Ya fara tuntubar shugabannin jam’iyya. Muna da shugabanni a matakin kasa, ya kamata ya gana da su."

Kara karanta wannan

Kuɗin da yawa: Gwamna Zulum ya faɗi biliyoyin Naira da ya kashe kan tsaro a 2025

"Dole ne a samu tattaunawa, ba ni in ba ka kafin mu karbe shi. Ya shigo ta hanyar da ya dace. Abin da kawai muke cewa kenan.".
"Dole ne a yi shawarwari da tattaunawa. Idan sharuddan sun yi wa jam’iyyar daɗi, za su karɓe shi. Amma idan ba mu fahimci niyyarsa ba, to nan ne matsalar take."
"Wannan ne ya sa kungiyoyi suke fitowa suna magana ko dai kan goyon baya ko a adawa da shigowarsa APC.”

- Rufus Bature

APC ta ki karbar Gwamna Mutfwang zuwa cikinta
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Rahotanni sun nua cewa banda “tsauraran sharuɗɗa” da wasu ke cewa an gindaya wa gwamnan, majiyoyi na kusa da shugaban APC na kasa sun ce Gwamna Mutfwang bai sanar da Nentawe cewa yana shirin sauya sheka zuwa APC ba.

An tsige shugaban APC a Cross River

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Cross River ta tsige shugabanta, Alphonsus Ogar Eba, daga kan mukaminsa.

Alphonsus Oga Eba ya rasa mukaminsa ne bayan mambobin majalisar zartarwar jam'iyyar na jiha (SEC) 30 cikin 32 sun kada ƙuri’ar rashin amincewa da shugabancinsa.

Kara karanta wannan

An bukaci gwamna ya gaggauta fita daga PDP a wata wasika da aka rubuta a Filato

Tsige shi na zuwa ne bayan watanni da dama ana zargin Eba da almudahana, mulkin kama-karya da kuma rufe sakateriyar jam’iyya na dogon lokaci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng