Fubara Ya Manta da Wike, Ya Fadi Wanda Ya Yi Silar Dawowar Shi Mulki

Fubara Ya Manta da Wike, Ya Fadi Wanda Ya Yi Silar Dawowar Shi Mulki

  1. Gwamna Siminalayi Fubara ya yi magana bayan dawowarsa ofis biyo bayan rikicin watanni shida a jihar
  2. Fubara ya danganta dawowarsa da tagomashin Shugaba Bola Tinubu yana mai cewa gwamnati ta koma cikakken aiki
  3. Ya tabbatar da cewa jihar za ta ci gaba da cika dukkan biyan kuɗi ga jami’ar Rivers, tare da gyara matsalolin gine-gine

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt - Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi godiya na musamman bayan dawo da shi kan kujerarsa.

Fubara ya ce cigaba da rike mukaminsa bayan dokar ta-baci ta watanni shida ya samu ne saboda “tagomashi na musamman” daga Shugaba Bola Tinubu.

Fubara ya yabawa Tinubu bayan dawo da shi mulki
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Siminalayi Fubara. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Alkawuran da Fubara ya dauka a Rivers

Fubara ya yi wannan bayani ne a yayin taron yaye ɗalibai karo na 37 da 38 na jami’ar da aka gudanar a Port Harcourt, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ɗaukar nauyin Jami’ar jihar Rivers gaba ɗaya don ƙarfafa bangaren ilimi a jihar.

Ya ce matsalolin da jami’ar ke fuskanta da dama ba za su taso ba da ace “ba a samu dan katsewar dimokradiyya a jihar ba.”

Ya ce:

“Kamar yadda kuka sani, an gabatar mana da rahoto. Amma duk ku san abin da ya faru a gwamnatarmu. Mun dawo ne saboda ikon Allah da kuma tagomashin Shugaban kasa.”
Fubara ya yiwa yan Rivers alkawura
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Source: Instagram

Bangaren da Fubara zai mayar da hankali

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta koma cikakken aiki, kuma duk korafe-korafen da jami’ar ta gabatar za a magance su nan ba da jimawa ba.

Ya bayyana cewa za a mayar da hankali kan gine-gine, tsaro, da jin dadin ma’aikata da ɗalibai, tare da gyara dukkan sassa musamman na harabar makarantu.

Fubara ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta shaidawa Tinubu lamarin rashin tsaro a jihar Kano

“Za mu ci gaba da cika dukkan hakkinmu na kuɗi ga jami'ar. Za a tabbatar da ingantattun gine-gine, tsaro, da jin dadin ɗalibai da malamai. Ilimi babban jarin gina kasa ne.”

Ya yabawa cigaban jami'ar wajen ingancin karatu, bincike da samar da shugabanni, yana mai shawartar jami’ar da ta kara zurfafa bincike don magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa a Rivers da Najeriya gaba ɗaya.

Gwamnan ya taya sababbin dalibai 13,242 murnar kammala karatu ciki har da takardun digiri, difloma da wasu shaidun karatu.

Ya kuma gode wa iyaye, masu kula da jami’ar da malamai kan jajircewar da suka yi wajen ganin ɗalibai sun kai ga nasara, cewar Daily Post.

Matakan da Fubara ya dauka bayan shiga ofis

Kun ji cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya dauki wasu matakai bayan Shugaba Bola Tinubu ya mayar da shi ofis.

A sabon matakin da ya dauka, Gwamnan ya kori kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati da ke aiki kafin a dakatar da shi.

Gwamna Fubara ya ce matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Koli da aka yanke inda ya bayyana cewa korar ta fara aiki nan take.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.