Tsohon Kakakin PDP na Kasa Ya Bi Sahun Gwamnoni 5, Ya Fice daga Jam'iyyar

Tsohon Kakakin PDP na Kasa Ya Bi Sahun Gwamnoni 5, Ya Fice daga Jam'iyyar

  • Bayan tsawon shekaru yana yi wa PDP hidima, Kola Ologbondiyan ya fice daga babbar jam'iyyara adawa ta kasa a ranar 5 ga watan Disamba, 2025
  • Ologbondiyanya ce ya yanke wannan shawara ne bayan nazari kan halin da PDP ke ciki da kuma yadda aka fara maida su gefe guda
  • Sauya shekar babban jigon na zuwa ne bayan gwamnoni biyar sun bar PDP tare da wasu manyan jiga-jigai a fadin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Manyan kusoshin da suka jima suna hidimatawa PDP na ci gaba da ficewa daga jam'iyyar yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.

Tsohon Sakatare Yaɗa Labarai na ƙasa a jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar bayan shekaru da dama yana aiki a manyan mukamai.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: 'Dan Majalisar Tarayya ya burma matsala, an kore shi daga YPP

Tsohon kakakin PDP, Kola Ologbondiyan.
Tsohon mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan Hoto: @KolaOlogbondiyan
Source: Twitter

Ologbondiyan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, tare da wasiƙar da ya aikawa shugaban jam’iyyar na mazabar Okekoko, ƙaramar hukumar Kabba/Bunu ta Jihar Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar ficewar tsohon kakakin PDP na kasa na dauke da kwanan watan 5 ga Disamba, 2025.

Ologbondiyan ya fita daga PDP

A cikin wasiƙar mai taken “Sanarwar murabus daga PDP”, Ologbondiyan ya ce ya yi nazari kan rawar da yake takawa a cikin jam’iyyar, sannan ya yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zai bar PDP:

Ya ce:

“Na yi nazari kan yadda ake bukatata da gudummuwar da nake ba jam’iyya kuma ga dukkan alamu, saboda dalilai na kaina, lokaci ya yi da zan yi bankwana da PDP. Don haka, daga yau na yi murabus daga zama mamba.”

Ya kuma gode wa jagorancin PDP bisa damar da suka ba shi ya yi aiki ga jam’iyyar da kuma Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Kuɗin da yawa: Gwamna Zulum ya faɗi biliyoyin Naira da ya kashe kan tsaro a 2025

Gwamnoni 5 sun bar jam'iyyar PDP

Ficewar Ologbondiyan na zuwa ne a wani lokaci da PDP ke fama da barazanar rugujewa sakamakon rigingimu da rikicin shugabanci da suka dabaibaye jam’iyyar a 2025.

Ana ganin dai wannan shekarar ta kasance mafi muni ga jam’iyyar tun kafuwarta, inda manyan jiga-jigai da dama suka fice zuwa jam’iyyar APC, cewar The Cable.

Daga cikin gwamnoni da suka bar PDP akwai Ademola Adeleke (Osun), Douye Diri (Bayelsa), Peter Mbah (Enugu), Sheriff Oborevwori (Delta) da Umo Eno (Akwa Ibom).

Tutar PDP.
Tutar babbar jam'iyyara adawa ta Najeriya, PDP Hoto: PDP Nigeria
Source: Facebook

Da yawa daga cikinsu sun danganta ficewarsu da rashin jituwar da ake samu a matakin shugabancin PDP ko kuma bukatar su daidaita da gwamnatin tarayya kafin 2027.

Tsohon mai magana da yawun PDP, Ologbondiyan ya zama na baya-bayan nan cikin jerin shugabanni da suka bar jam’iyyar yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027.

PDP ta yi magana kan ficewar Gwamna Adeleke

A wani rahoton, kun ji cewa Kabiru Tanimu Turaki, wanda yake shugaban bangaren PDP na kasa, ya yi magana kan ficewar Gwamna Ademola Adeleke daga cikin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Da gaske an kama Wike a Faransa? Ministan ya fadi halin da yake ciki

Turaki ya jaddada cewa har kawo yanzu PDP ba ta samu wata takarda a hukumance daga Gwamna Ademola Adeleke ba game da ficewarsa daga jam’iyyar.

Shugaban PDP na kasa ya ce Gwamna Adeleke yana da ‘yanci a kundin tsarin mulki na kasa na barin jam’iyya ko ci gaba da zama cikinta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262