Jonathan Ya Samu Gargadi kan Yin Takara, An Fadi Manufar Masu Son Ya Gwabza da Tinubu a 2027
- Wasu na ganin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan zai sake jaraba sa'arsa wajen neman shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2027
- Shugaban jam''iyyar ZLP na kasa, Dan Nwanyanwu OFR, ya fito ya gargadi Jonathan kan biyewa masu son ganin ya kara da Shugaba Bola Tinubu
- Nwanyanwu ya nuna cewa masu zuga tsohon shugaban kasar ba mutanen da za a yadda da su ba ne kuma akwai manufar da suke son cimmawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar ZLP na kasa, Dan Nwanyanwu, ya ja kunnen tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.
Dan Nwanyanwu ya gargadi Goodluck Jonathan da ya guji tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Source: Facebook
Shugaban na ZLP ya bayyana hakan ne yayin wata hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma’a, 5 ga watan Nuwamban 2025.
Wace shawara aka ba Jonathan kan 2027?
Nwanyanwu ya ce mutanen da suke zuga Jonathan ya tsaya takara yanzu su ne wadanda suka yi aikin kawar da shi a lokacin da yake mulki, kuma suna yi ne don son zuciya.
Ya goyi bayan ra’ayin uwargidan tsohon shugaban kasar, Madam Patience Jonathan, wadda take adawa da mijinta ya sake tsayawa takara.
“Ban yi magana da Shugaba Jonathan ba tukuna. Ina shirin ganinsa nan ba da jimawa ba, amma ina ganin ya kamata ya yi hakuri.”
“Ina tare da Madam Patience saboda mutanen da suke kira gare shi yanzu su ne suka ci amanarsa a baya. Mutum nagari, wanda ya yi manufofi masu kyau ga Najeriya."
"Sun ci amanarsa, yanzu kuma suna son amfani da shi ne don wanke kura-kuransu.”
- Dan Nwanyanwu
Ana hasashen Jonathan zai fito takara
Jonathan, wanda ya mulki Najeriya daga 2011 zuwa 2015, ya fara shugabanci bayan rasuwar shugaba Umaru Musa Yar’Adua, inda ya karɓi ragamar mulki daga matsayin mataimaki.

Kara karanta wannan
Chibok: Fadar shugaban kasa ta yi magana da aka dauko kalaman da Tinubu ya yi a 2014
Yayin da zaben 2027 ke matsowa, ana cigaba da kiraye-kiraye daga wasu ‘yan Najeriya da shugabannin PDP, inda suke neman Jonathan ya tsaya takara, suna cewa kwarewarsa ta cancanci a sake ba shi dama.

Source: Facebook
Sai dai har yanzu tsohon shugaban bai bayyana niyyarsa ta tsayawa takara ba, kuma ya sha bayyana cewa bai da shirin yin hakan a yanzu.
Tun bayan barin mulki, Jonathan ya mayar da hankali ne kan aikin diflomasiyya, sa ido kan zabe, da aikin samar da zaman lafiya a kasashen Afirka.
Dalilin Jonathan na yin baya da siyasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya dauko batun dalilin da ya sanya ya ja baya daga shiga al'amuran siyasar Najeriya.
Goodluck Jonathan ya bayyana cewa rawar da yake takawa a matsayin mamba a kungiyar West African Elders Forum (WAEF) na bukatar tsantsar rashin nuna goyon baya ga wani bangare.
Tsohon shugaban kasar ya nuna cewa zama mamba na WAEF yana zuwa ne da sharadi ɗaya mai tsauri, ba za ka ci gaba da shiga siyasa ta jam’iyya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
