Wata Sabuwa: Jam'iyyar APC Ta Haramtawa Manyan Ƴan Siyasa 6 Shiga Takarar Gwamna
- Kwamitin tantancewa na APC ya hana Iyiola Omisore da wasu 'yan takara shida shiga zaben fitar da gwani na zaben gwamna a Osun
- Rahoton kwamitin ya nuna cewa wadanda aka haramta wa neman takarar sun gaza gabatar da wasu muhimman takardu yayin tantancewa
- APC ta ce mutane biyu ne yanzu kawai suka tsallake tantancewar, inda za su fafata a zaben fitar da gwani da za a gudanar nan gaba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Kwamitin tantance ‘yan takarar gwamna na APC ya hana tsohon sakataren jam’iyyar na kasa, Iyiola Omisore, da wasu mutum shida shiga zaben fitar da gwani.
APC ta hana manyan 'yan siyasar shida damar shiga zaben fitar da gwanin gwamnan jihar Osun da aka shirya gudanarwa ranar 13 ga Disamba, 2025.

Source: Twitter
APC ta hana mutane 6 shiga takarar gwamna
Wannan mataki ya biyo bayan gano kurakurai da gibin takardu a cikin bayanan da suka mika wajen neman tikitin jam’iyyar, in ji rahoton jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton kwamitin, ya nuna cewa akwai bukatar manyan jiga-jigan jam’iyyar su yi sulhu domin kaucewa rikice-rikicen cikin gida yayin da zaben gwamna ke kara matsowa.
Kwamitin, karkashin jagorancin Obinna Uzoh, Esq., ya kammala tantance masu neman takarar a ranar 4 ga Disamba 2025, sannan ya mika rahotonsa ga NWC na jam’iyya a Abuja.
A cewar rahoton, dukkan wadanda aka cire sun kasa gabatar da shaidar samun goyon baya daga akalla mambobi biyar na kowace karamar hukuma ba, wanda kundin tsarin mulki na jam’iyyar ya tanada.
Wannan kuskure ya sanya Sanata Omisore tare da Babatunde Oralusi, Oyedotun Babayemi, Dr. Akin Ogunbiyi, Benedict Alabi, Adegoke Rasheed Okiki da Babajide Omoworare sun fadi tantancewar gaba daya.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
'Yan takara 2 da APC ta tantance a Osun
Kwamitin ya bayyana cewa kawai mutum biyu ne cikin ‘yan takarar suka cika dukkan sharuddan jam’iyyar, kamar yadda rahoton Tribune ya nuna.
Wadanda suka tsallake tantancewar su ne Mulikat Abiola Jimoh da Munirudeen Bola Oyebamiji, kuma yanzu za su je matakin zaben fitar da gwani.
Kwamitin ya bayyana cewa ya gudanar da aikinsa ta hanyar bincike mai zurfi na takardu da kuma tattaunawa kai tsaye da kowanne dan takara don tantance ingancinsu da cikakken shiri na tafiyar da mulki.

Source: Original
Rikici ya yi kamari a APC reshen Osun
Rahoton ya kuma tabbatar da cewa akwai korafi daga kungiyar APC-RG ta jihar Osun, wadda ta bukaci a dakatar da wasu daga cikin ‘yan takarar saboda rashin cika sharuddan kundin tsarin jam’iyya.
Haka kuma kwamitin ya bayyana cewa jam’iyyar APC a Osun na fama da matsalolin rarrabuwar kai mai tsanani, wanda zai iya zama illa ga jam’iyyar a zaben jihar na 2026 idan ba a shawo kansu ba.
Don haka, rahoton ya ba da shawarar cewa shugabancin jam’iyya na kasa ya hanzarta kafa kwamitin sulhu domin hada kan bangarori daban-daban da ke takaddama a cikin jihar.
Gwamnan Osun ya fice daga jam'iyyar PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya fara laluben jam'iyyar da zai koma domin samun tikitin takara a zaben 2026.
A wata sanarwa da Gwamna Adeleke ya fitar yau Litinin, 1 ga watan Disamba, 2025, ya ce ya bar PDP ne saboda rikicin jam'iyyar da ya ki ci ya ki cinyewa.
Wasu majiyoyi sun ce Gwamna Adeleke ya fara tunanin komawa jam'iyyar Accord Party domin tsayawa takarar gwamna karo na biyu a 2026.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

