Rivers: Yan Majalisa 16 Sun Watsar da PDP, Sun Zabi Kasancewa a APC
- Mambobi 16 na majalisar dokokin Rivers sun fice daga PDP da Gwamna Siminalayi Fubara ya ke cikinta
- 'Yan majalisar dokokin jihar sun bayyana matsayarsu ne a yau Juma'a 5 ga watan Disambar 2025 da muke ciki
- Kakakin majalisa Martin Amaewhule shi ya jagoranci sauya shekar yan majalisar inda ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Yan majalisar dokokin jihar Rivers sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Mambobin majalsiar 16 sun sanar da yanke shawarar shiga jam'iyyar APC mai adawa, a wani sauyin siyasa da ya girgiza majalisar.

Source: Twitter
Rivers: 'Yan majalisa sun bar PDP zuwa APC
Kakakin majalisar, Martin Amaewhule, ne ya bayyana sauya shekar a zaman majalisar da aka yi a ranar Juma’a 5 ga watan Disambar 2025, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amaewhule ya ce shi ma ya yanke shawarar barin jam’iyyar PDP zuwa APC inda ya yabawa Bola Tinubu.
A cewarsa:
“Abokaina 'yan majalisa, ina farin cikin sanar da ku cewa na rubuta wa shugaban gundumata na PDP cewa na fice daga jam’iyyar. APC ce sabuwar jam’iyyata yanzu.”
Amaewhule ya kara da cewa zai yi duk abin da ya dace domin samun katin APC cikin gaggawa, yana mai jaddada cewa yanzu haka ya zama cikakken mamba na jam’iyyar domin ya hada kai da Shugaba Tinubu.
Ya ce:
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana yi wa kasa aiki sosai. Yana yakar matsalar tsaro kai tsaye. Ya nuna kauna ga jama’ar Rivers. Shugaban kasa yana taimaka wa mutanen Rivers su samu gurbi a gwamnatin tarayya.”

Source: Facebook
Dalilin barin mambobin majalisar Rivers PDP
Kakakin ya bayyana rabuwar kai a PDP a matsayin babban dalilin da ya sa suka yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar, kamar yadda Channels ta ruwaito.
Sauran mambobin majalisar da suka koma APC sun hada da: Dumle Maol, Major Jack, Linda Stewart, Franklin Nwabochi, Azeru Opara, Smart Adoki da Enemi George.
Sauran sun hada da Solomon Wami, Igwe Aforji, Tekena Wellington, Looloo Opuende, Peter Abbey, Arnold Dennis, Chimezie Nwankwo, da Ofiks Kabang.
A baya-bayan nan, majalisar dokokin Rivers mai mambobi 32 ta yanke shawarar amincewa ga Shugaba Tinubu, tare da rokon shi da ya sake tsayawa takara.
A ranar 18 ga Maris, Shugaba Tinubu ya kakaba doka ta-ɓaci a jihar Rivers saboda rikicin siyasa da rashin kwanciyar hankali da suka ci gaba da ta’azzara a jihar.
Haka kuma ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin majalisa na tsawon watanni shida.
An fara rigima tsakanin Fubara da yaran Wike
A baya, mun ba ku labarin cewa an fara samun sabani tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin Rivers bayan wata biyu da dawowa dimokiradiyya.
Majalisar ta zargi gwamnatin Fubara da watsi da makarantu tare da tambayar yadda aka yi da N600bn da aka bari a baitul-malin jihar.
Gwamna Simi Fubara ya mayar da martani cewa ba zai dauki ma’aikata don biyan bukatun siyasa ba, sai dai bisa bukatar jihar kawai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


