Ana Wata ga Wata: Majalisar SEC Ta Yi Zama, An Tsige Shugaban Jam'iyyar APC
- Mambobi 30 cikin 32 na majalisar zartarwar APC a jihar Cross River sun kada kuri'ar tsige shugaban jam'iyya, Alphonsus Eba
- Shugabannin APC sun zargi Eba da almundahana, danniya, da rufe sakateriyar jam’iyya na watanni ba tare da kawo wani dalili ba
- Mataimakin shugaban APC ya dare kujerar shugaba na wucin gadi, yayin da ya yi alƙawarin sulhu da sake farfado da ayyukan jam’iyya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Cross River - Jam’iyyar APC reshen jihar Cross River ta tsige shugabanta na jiha, Alphonsus Ogar Eba, a ranar Alhamis, 4 ga watan Disamba, 2025.
An tsige shugaban APC din ne bayan mambobin majalisar zartarwar jam'iyyar na jiha (SEC) 30 cikin 32 sun kada ƙuri’ar rashin amincewa da shugabancinsa.

Source: Twitter
An tsige shugaban jam'iyyar APC
Wannan mataki ya zo ne bayan watanni da dama ana zargin Eba da almudahana, mulki kama-karya da kuma rufe sakateriyar jam’iyya na dogon lokaci, in ji rahoton Vanguard.
Zarge-zargen da ake yi wa shugaban APC na Cross River sun haifar da mummunar alaka da rikici mai tsanani a jam’iyyar, lamarin da ya tilasta manyan jiga-jigai da shugabanni na ƙananan hukumomi daukar matakin gaggawa domin “tsare mutuncin jam’iyya.
Manya a jam’iyyar sun bayyana cewa Eba ya karya amana ta hanyar gudanar da harkokin jam’iyya ba tare da yin bayani ga mambobi ba, tare da rufe sakatariya, lamarin da ya gurgunta duk ayyukan ofis.
Shugaban APC na Boki, Chief Kelvin Njong, wanda kuma shi ne mai magana da yawun shugabannin kananan hukumomi 18, ya ce an kai korafe-korafe masu nauyi ga uwar jam’iyya ta kasa kafin daukar matakin tsige Eba.
APC: An nada shugaban rikon kwarya
Kelvin Njong ya ce wannan hukunci ya biyo bayan dogon nazari da tattaunawa, kuma ya zama dole domin “tsayar da rikicin da ke neman tarwatsa jam’iyya.”
Bayan tsige Eba, majalisar SEC ta tabbatar da cewa Ntufam Ekum Ekok Ojogu, mataimakin shugaban jam’iyyar, zai rike ragamar shugabanci a matsayin rikon kwarya.
Rahoton The Nation ya nuna cewa, majalisar jiha ta APC a Cross River ta dauki wannan mataki ne bisa tanadin sashe na 17(6) na kundin tsarin jam’iyyar.
An kuma rahoto cewa tuni Ojogu ya yi rantsuwar kama aiki, inda ya yi alkawarin farfado da jam'iyyar, bude sakatariya, da kuma yin sulhu da dukkan masu ƙorafi.

Source: Original
Kokarin daidaita rikice-rikicen APC
Shugaban riko na APC a Cross River, Ojogu ya ce:
“Lokaci ne da za mu ajiya duk wata gaba, mu farfado da jam’iyyar mu. Duk wani hakkinku da aka danne, za a biya. Kofa ta a bude take a gare ku, haka ma layukan wayata.”
Ya gode wa jiga-jigan jam'iyyar saboda jajircewar da suka nuna duk da rikicin da ya daɗe yana gurgunta jam'iyyar, yana mai cewa zai yi aiki kafada da kafada da Gwamna Bassey Otu.
Bayan rantsuwar, shugabannin reshen jihar da na kananan hukumomi suka shiga taron sirri domin tsara sauye-sauyen da zasu biyo baya, tare da shirya rahoto na musamman da za a mikawa uwar jam’iyya a Abuja.
An maka shugaban jam'iyyar APC a kotu
A wani labari, mun ruwaito cewa, rikicin siyasa ya mamaye APC a Zamfara bayan an maka shugaban jam’iyya na jihar, Tukur Danfulani, a gaban kotu.
Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar guda uku ne suka maka Tukur Danfulani a gaban babbar kotu da ke Gusau, bayan sanarwar dakatar da su da aka yi daga APC.
A cikin karar da suka shigar ranar 14 ga Nuwamba 2025, sun bukaci kotu ta, tabbatar da cewa su duka halastattun ’yan APC ne kuma a soke dakatarwar da aka yi masu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


