APC Ta Samu Koma Baya a Zamfara Ana Rade Radin Gwamnan PDP Zai Koma Cikinta

APC Ta Samu Koma Baya a Zamfara Ana Rade Radin Gwamnan PDP Zai Koma Cikinta

  • Jam'iyyar APC mai adawa a Zamfara ta gamu da cikas bayan wasu mambobinta guda biyu a majalisar dokokin jiha sun yi murabus daga cikinta
  • Mambobin guda biyu sun sanar da raba gari da APC ne a cikin wasiku daba-daban da suka aikawa shugaban majalisar dokokin, Bilyaminu Moriki
  • Sun bayyana cewa lokaci ya yi da za su yanke alakar da ke tsakaninsu da APC saboda abin da suka kira rashin jagoranci mai kyau a jam'iyyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Wasu mambobi biyu na majalisar dokokin jihar Zamfara sun fice daga jam’iyyar APC mai adawa.

Mambobin majalisar dokokin sun danganta matakin nasu da rikice-rikicen cikin gida da matsalolin jagoranci da suka dabaibaye jam’iyyar APC.

APC ta samu koma baya a jihar Zamfara
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da tambarin jam'iyyar Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa mambobin majalisar dokokin sun sanar da ficewarsu ne a cikin wata wasika da suka aikawa shugaban majalisar.

Kara karanta wannan

An fara sabon takun saka tsakanin gwamna Fubara da yaran Wike a majalisar Rivers

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan majalisa 2 sun fice daga APC a Zamfara

Mambobin su ne Shamsudeen Hassan Masko mai wakiltar Talata Mafara ta Arewa da Nura Dahiru mai wakiltar Birnin Magaji.

Sun dai bayyana murabus ɗinsu ne a cikin takardu daban-daban da suka aika wa shugaban majalisar, dauke da ranar 3 ga watan Disamban 2025.

An karanta wasikun a zaman majalisar ta hannun shugabanta, Bilyaminu Moriki, a ranar Alhamis, 4 ga watan Disamban 2025.

Meyasa 'yan majalisar suka fice daga APC?

Hassan Basko ya ce ya yanke shawarar ficewa ne saboda dogon lokaci ana fama da rikice-rikice, rarrabuwar kai, rashin ingantaccen jagoranci da kuma watsi da mambobi daga matakin ƙananan hukumomi har zuwa jiha.

Ya kara da cewa kasancewa cikin APC bai dace da akidarsa ko muradun al’ummar da yake wakilta ba.

“Bayan dogon nazari a kan al’amuran jam’iyya, matsaloli, rarabuwar kai da kalubalen shugabanci daga kananan hukumomi zuwa matakin jiha, na ga ya dace na koma gefe na daina shiga harkokin jam’iyyar."

Kara karanta wannan

Wasu manyan matsaloli 5 da Janar Musa zai fuskanta idan ya zama ministan tsaro

- Hassan Shamsudeen Basko

Shi kuma Nura Dahiru ya bayyana cewa barin APC zai ba shi damar yin gwagwarmayar da za ta fi wakiltar bukatu da muradun mutanen da ya ke wakilta,.jaridar Vanguard ta dauko labarin.

Dukkan su sun gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba su tun farkon zuwansu siyasa, tare da neman a ɗauki wasikunsu a matsayin sahihiyar sanarwar ficewarsu.

'Yan majalisar APC sun koma APC a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wace jam'iyya suka koma?

Bayan ficewarsa, Nura Dahiru ya bayyana shigarsa jam’iyyar PDP a jihar Zamfara kai tsaye.

Hakazalika, shi ma Shamsudeen Hassan Basko ya koma jam'iyyar PDP mai mulki a jihar tun bayan zaben da aka yi a farkon shekarar 2023.

An bukaci Gwamna Mutfwang ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ana ci gaba da kira ga gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Kungiyar magoya bayan PDP ta Coalition of PDP Supporters reshen jjhar Filato ta shiga layin wadanda ke ganin ya kamata Gwamna Mutfwang ya koma APC ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Bayan an ceto daliban Kebbi, ƴan siyasa fiye da 1500 sun fice daga PDP zuwa APC

Shugaban ƙungiyar, Hon. Christopher Dajem, ya bayyana haka ne yayin mika wa gwamnan wasiƙar buƙatar sauya sheka a Fadar Gwamnati da ke Little Rayfield, Jos.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng