Kasafin 2025: Cacar Baki Ta Barke tsakanin Tsohon Kwamishina da Gwamnatin Kano

Kasafin 2025: Cacar Baki Ta Barke tsakanin Tsohon Kwamishina da Gwamnatin Kano

  • Tsohon kwamishinan Abdullahi Ganduje, Muhammad Garba ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da gaza aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025
  • Ya ce gwammatin NNPP mai ci ta cika mutane da surutu amma rahoton ayyukan kasafin kudi ya nuna gazawarta daga Janairu zuwa Satumba, 2025
  • Gwamnatin Kano ta tanka masa cikin gaggawa, tana mai cewa zarge-zargen da ya yi siyasa ce kawai amma babu hujja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - An fara musayar yawu tsakanin tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Kano, Muhammad Garba, da gwamnatin NNPP ta Abba Kabir Yusuf kan batun aiwatar da kasafin kudin 2025.

Muhammad Garda, wanda ya yi aiki a gwamnatin Abdullahi Ganduje, ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da cika mutane da surutu, ba tare da aiwatar da aiki a zahiri ba.

Kara karanta wannan

Shugaban gwamnonin Arewa ya ce sun ga uwar bari game da rashin tsaro

Gwamna Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnati Hoto; Sanusi Bature
Source: Facebook

A ruwayar Leadership, Garba ya ce rahoton nazarin kasafin kuɗi ya nuna cewa gwamnatin Kano mai ci ba ta aiwatar da 40% na ayyukan kasafin ba zuwa watan Satumba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Ganduje ya dura kan gwamnatin Kano

Garba ya yi zargin cewa Hukumar Ruwa ta Kano, duk da samun N5.6bn don ayyukan ci gaba, “ba ta kashe ko sisin kwabo ba” a lokacin, duk da matsalar ƙarancin ruwa da ake fama da ita a jihar.

“Gwamnati ta ayyana dokar ta-baci kan ruwan sha, amma ba ta saka ko kashi 1 cikin 100 na kuɗin da aka ware ba,” in ji shi.

Ya kuma zargi gwamnati da watsi da aikin tashar wuta ta Tiga Hydropower, wanda ya ce hakan ya tilasta ci gaba da siyan wutar lantarki daga KEDCO kan tsadar kuɗi.

A bangaren ilimi, tsohon kwamishinan ya ce duk da fannin ya samu kaso mafi tsoka a kasafin 2025 na Kano, amma batun aiwatarwa ya zama abin takaici.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati ta yi bayani kan dokar hana acaba, an yi sassauci a wasu yankuna

A bangaren lafiya, Garba ya ce an kashe N7.9bn daga cikin N65.7bn kacal zuwa Satumba 2025, yana mai cewa rashin zuba jari a kiwon lafiya da ruwan sha “na janyo mutuwar jama’a."

Ya tabo bangaren gina tituna, sannan ya kuma soki kasafin kuɗin 2026 na sama da Naira tiriliyan daya, yana cewa:

“Gwamnati da ba ta iya aiwatar da rabin kasafin kuɗi bana ba, ta yaya za ta yi kasafin fiye da Naira tiriliyan ɗaya?”

Gwamnatin jihar Kano ta maida martani

Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Kano, Umar Haruna Muhammad Doguwa, ya mayar da martani, yana mai cewa zargin Garba siyasa ce kawai amma ba shi da hujja.

"Ba lokaci guda ake fitar da kudin kasafi ba, yawancin ayyuka na kankama ne a kashin shekara na uku watau Q3 da na karshe, Q4."

Ya ce gwamnati Abba ta gaji bashin sama da N2bn na KEDCO daga gwamnatin da ta gabata, wanda hakan ya hana tashoshin ruwa aiki sabida rashin wutar lantarki.

Muhammad Garba da Gwamna Abba.
Tsohon kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano Hoto: Garba Muhammad, Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Doguwa ya bayyana wasu ayyuka da ke gudana yanzu haka kamar gyaran manyan tashoshin ruwa na Tamburawa, Challawa, Watari, biyan kudin wuta a kan lokaci da sauransu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

Kwamishinan ya ce zarge-zargen da Garba ya yi tsohon salon siyasa ne da aka daina ya yi, inda ya bukaci jama'a su jira hakikanin rahoton 2025, in ji rahoton Guardian.

Gwamnatin Kano ta nemi kama Ganduje

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta nuna damuwa kan kalaman tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje da shirinsa na kafa Hisbah mai zaman kanta

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nemi a kama kuma a binciki tsohon gwamnan bisa zargin yin maganganun da ka iya tayar da tarzoma a Kano.

Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce maganganun na iya dagula kokarin gwamnatin tarayya da ta jiha wajen samar da tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262