Adeleke: Martanin PDP bayan Wani Gwamnan Ya Sake Ficewa daga Jam'iyyar
- Gwamnan jihar Osun, Mai girma Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Shugaban tsagin jam'iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki, ya fito ya yi magana kan matakin da gwamnan ya dauka na raba gari da jam'iyyar
- Turaki ya ce a bakin duniya suka tsinci labarin ficewar gwamnan na jihar Osun domin bai sanar da su a hukumance cewa ya fice daga PDP ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kabiru Tanimu Turaki, wanda yake shugaban bangaren PDP na kasa, ya yi magana kan ficewar Gwamna Ademola Adeleke daga cikin jam'iyyar.
Kabiru Tanimu Turaki SAN ya ce PDP ba ta samu wata takarda a hukumance daga Gwamna Ademola Adeleke ba game da ficewarsa daga jam’iyyar.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai bayan taron kwamitin amintattu na kasa (NWC) na PDP, a birnin Abuja.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Talata ne aka ji Gwamna Adeleke ya fice daga PDP, inda ya danganta matakin da rikicin da ya dade yana addabar jam’iyyar.
Me PDP ta ce kan ficewar Gwamna Adeleke?
Kabiru Tanimu Turaki ya ce Adeleke yana da ‘yanci a kundin tsarin mulki na barin jam’iyya ko ci gaba da zama cikinta, tashar Channels tv ta kawo labarin.
Ya ce PDP ta ji labarin ficewar ne ta kafafen yada labarai, amma ba ta samu wata takarda kai tsaye daga gwamnan ba.
“Mun ga wata takarda a kafafen sada zumunta da ake cewa daga gare shi ta fito, amma har yanzu ba mu samu wata sanarwa a hukumance da ta nuna ya bar jam’iyya ba."
- Kabiru Tanimu Turaki
Ya bayyana cewa sunan Adeleke har yanzu yana cikin jerin masu neman takarar gwamna a Osun.
Kabiru Tanimu Turaki ya ce jam’iyyar za ta jira rahoton jami’anta a wurin zaben fitar da gwani don tabbatar da ko gwamnan ya janye daga takara ko kuwa yana nan daram.

Kara karanta wannan
Magana ta fara fitowa, An Ji Dalilan da suka jawo Gwamna Adeleke ya fita daga PDP
“A gare mu, ko da takardar da ke yawo gaskiya ce, Gwamna Adeleke, kamar kowane ɗan Najeriya, yana da cikakken ‘yancin shiga ko barin kowace jam’iyya,”
- Kabiru Tanimu Turaki

Source: Twitter
PDP ta ce jama'a na goyon bayanta
Kabiru Tanimu Turaki ya kara da cewa karfin PDP yana hannun talakawa da magoya baya ne, ba a hannun manyan jami’an gwamnati da ke barin jam’iyya ba.
A cewarsa, ficewar gwamnonin wasu jihohi ba ta rage wa jam’iyyar karbuwa a kasa ba.
“Mutanenmu sun tsaya tsayin daka da mu, kuma da ikon Allah idan lokacin zabe ya yi, za su nuna cewa PDP tana nan daram."
- Kabiru Tanimu Turaki
Jam'iyyar PDP ta roki Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta mika kokon bararta ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
PDP ta bukaci Shugaba Tinubu da ya ceto adawa a kasar nan kamar yadda ya ceto jagoran 'yan adawa na kasar Guinea-Bissau.
Ta bayyana cewa bai kamata shugaban kasar ya zura ido ya bar wasu na kusa da shi na kunno wutar rigingimu a cikin jam'iyyun adawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng