Jagora a ADC Ya Fara Karaya game da Aniyarsu na Korar Tinubu daga Aso Rock

Jagora a ADC Ya Fara Karaya game da Aniyarsu na Korar Tinubu daga Aso Rock

  • Jagora a jam'iyyar ADC, Dele Momodu ya bayyana takaici saboda 'yan adawa suka gaza hada kawunansu gabanin zaben 2027 mai zuwa
  • Momodu ya bayyana cewa yana mamakin yadda aka yi manyan hadakar adawa su ka rarrabu yayin da ake kokarin fitar da Bola Tinubu daga ofis
  • Ya yi gargadin cewa dole sai an yi rubdugu wajen goyon bayan Atiku Abubakar, domin shi kadai ne zai iya raba APC da mulkin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shahararren ɗan siyasa a jam’iyyar ADC kuma fitaccen marubuci, Dele Momodu, ya yi tsokaci kan siyasar Najeriya da shirin tunkarar babban zabe mai zuwa.

Ya bayyana cewa mafi yawan ’yan takarar adawa da ke harin kujerar shugaban kasa a 2027 na nuna cewa babu hadin kai sam a tafiyarsu.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro

Dele Momodu ya ce ba a shirya fitar da Tinubu daga ofis
Dele Momodu tare da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

Momodu ya wallafa bayanansa ne a shafinsa na X, yana mai cewa ba kasafai ake doke shugaban kasa mai ci ba sai da kyakkyawan shiri domin a tabbata an samu damar kawar da gwamanti a hanyar dimokuradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dele Momodu ya soki 'yan jam'iyyar ADC

A cewarsa, abin mamaki ne yadda wasu ’yan takara ke tunanin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu alhali ba su ma fara tattaunawa da juna ba, balle su gina tafiyar da za a ta iya jijjiga gwamnati mai ci.

Dele Momodu na son a marawa Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya ce:

“Ina mamakin yadda wasu ’yan takarar adawa ke tunanin kayar da Tinubu a 2027… alhali ba su ma hadu ba domin su tsara manufa ɗaya ba.”

Momodu ya jaddada cewa siyasar neman kujerar shugaban kasa ba wuri ne na wasa ko rawar kai ba, inda ya ce nasarar doke shugaban kasa mai mulki tana buƙatar a hada karfi domin gudanar da aikin da ya kamata.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

Momodu na son a marawa Atiku baya

A wasu kalaman nasa, Dele Momodu ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, yana mai cewa shi ne kaɗai ɗan adawar da yake kan tsarin da zai iya raba Tinubu da mulki.

Ya ce:

“Shi kaɗai ne jagoran adawa da ke bin tsari, kuma wannan shi ne yunƙurinsa na bakwai. Ya san yadda ake yin siyasar gaske domin ya zama mai tsayawa tsayin-daka.”
“Nasara ba ta zuwa da farin jini a kafafen sada zumunta kawai. Ana bukatar kuɗi masu yawan gaske"

Jam'iyyar ADC ta birkice a Adamawa

A baya, mun wallafa cewa rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar hamayya ta ADC a Jihar Adamawa ya kara kamari a ranar Litinin, inda aka samu baraka mai zafi tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa Mataimakin Shugaban ADC na Kasa (Arewa maso Gabas), Injiniya Babachir David Lawal, da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Adamawa, Shehu Yohanna, sun samu sabani.

Kara karanta wannan

Sace dalibai a Neja: Ribadu ya bada tabbaci bayan ganawa da shugabannin Kiristoci

Shehu Yohanna, wanda ake ganin yana da goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, yana daga cikin mutum uku da ke ikirarin shugabancin jam'iyyar a Adamawa daga Arewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng