Atiku Ya Gana da Shugabannin ADC, Ya Fada Masu Shirin da Za Su Yi Gabanin 2027
- 'Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gana da shugabannin ADC na jihohi 36 da Abuja bayan shigarsa jam’iyyar
- Shugabannin ADC sun ce sun yi farin cikin karɓar Atiku a matsayin mamba, inda suka nuna aniyarsu ta mara masa baya
- Atiku ya yaba wa jagororin ADC bisa jajircewarsu, ya kuma bukaci magoya bayansa su yi rajista a jam'iyyar gabanin 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Litinin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gana da shugabannin jam’iyyar ADC na jihohi 36 da kuma na Abuja, a gidansa da ke Abuja.
Shugabannin ADC sun ziyarci dan takarar shugaban kasar na PDP a zabe 2023 ne bisa jagorancin shugaban jam'iyyar na Kogi, Ogga Kingsley.

Source: Twitter
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Atiku ya ce tawagar ta ziyarce shi domin taya shi murnar zama sabon dan jam’iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin ADC sun ziyarci Atiku Abubakar
A cewar Atiku, Kingsley ya bayyana cewa shugabannin ADC na jihohi suna farin cikin karɓar shi a jam’iyyar, musamman ganin rawar da yake takawa a siyasar Najeriya.
Atiku ya ce shigarsa jam’iyyar na zuwa a lokacin da ake bukatar haɗin kai da yunkuri na gaggawa domin farfado da Najeriya.
Ya yi kira ga sauran ‘yan jam'iyyun adawa da ke cikin sabon tsarin haɗakar da su kammala rajistarsu, yana mai cewa:
“Ina farin cikin ganin cewa shugabannin jam’iyyar a matakin jiha suna tunani da hangen nesa kan makomar Najeriya. Mun kuduri niyyar yin mulki domin samar wa Najeriya tsaro, karfafa hadin kai da cigaban kasa."
“Lokacin adawa ya soma” — Atiku
Ya yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki “na hanyar rusa kasar”, yana mai cewa jam’iyyar hadaka ta ADC ce kawai za ta iya dakile hakan yanzu.
Atiku ya bayyana shigarsa jam’iyyar ADC a hukumance ne a mazabarsa ta Jada 1 da ke jihar Adamawa, inda ya karɓi katin zama mamba.
Ya ce shigarsa ADC alama ce da ke nuna cewa “an soma babbar adawa a kasar nan,” yayin da ya kuma bukaci magoya bayansa a duk fadin kasa su bi sahu su yi rajista a jam’iyyar.

Source: Twitter
Dalilin da ya sa Atiku ya bar PDP
A watan Yuli, Atiku ya sanar da ficewarsa daga PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta kauce daga tushen da aka kafa ta a kai.
Ya bayyana ficewar a matsayin abin takaici saboda rashin shawo kan sabanin cikin gida da ya daɗe yana ta’azzara, in ji rahoton Punch.
Atiku ya ce lokaci ya yi da za a samar da sabuwar tafiya, yana mai nuni da cewa hadakar 'yan adawa na da niyyar gabatar da wata sabuwar dama ta siyasa ga ’yan Najeriya gabanin 2027.
Atiku ya fara zawarci abokan takara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bangaren tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a cikin jam’iyyar ADC ya fara shirin zaben 2027.
Atiku ya fra duba mutanen da yake so su yi takara tare daga Kudancin Najeriya, ciki har da tsohon abokin takararsa a zaben 2019.
Wata majiya ta rahoto cewa idan Peter Obi ya ki amincewa ya tsaya tare da Atiku, to Atiku zai koma neman tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

