"Na Gaji haka ban" Gwamna Ya Mika Takardar Murabus, Ya Fice daga Jam'iyyar PDP
- Ta tabbata Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya fara laluben jam'iyyar da zai koma domin samun tikitin takara a zaben 2026
- A wata sanarwa da Gwamna Adeleke ya fitar yau Litinin, 1 ga watan Disamba, 2025, ya ce ya bar PDP ne saboda rikicin jam'iyyar da ya ki ci ya ki cinyewa
- Wasu majiyoyi sun ce Gwamna Adeleke ya fara tunanin komawa jam'iyyar Accord Party domin tsayawa takarar gwamna karo na biyu a 2026
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Bayan tsawon lokaci ana rade-radi, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tatttara kayansa ya fice daga jam'iyyar PDP.
Mai Magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya tabbatar da ficewar Adeleke daga PDP a cikin wata sanarwa da ya fitar daren Litinin, 1 ga watan Disamba, 2025.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Gwamna ya sanya dokar hana fita ta awa 24 bayan barkewar rikici

Source: Twitter
Gwamna Adeleke ya wallafa wannan sanarwa a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa ya fice daga PDP tun a ranar 4 ga watan Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa Gwamna Adeleke ya bar PDP?
Mai girma gwamnan ya aika wasikar murabus ɗinsa daga jam'iyyar ga Shugaban PDP na Mazaba ta 2, Sagba Abogunde, a karamar hukumar Ede ta Arewa, Jihar Osun.
Gwamna Adeleke ya danganta dalilin barin jam’iyyar ga rikicin da ya addabi shugabancin PDP ta ƙasa.
Ya rubuta cewa:
“Saboda rikicin da ke dagula al'amurran shugabannin PDP na ƙasa a yanzu, ina sanar da ficewata daga jam’iyyar PDP nan take ba tare da ba ta lokaci ba."
Gwamna Adeleke ya gode wa jam'iyyar PDP
Gwamna Adeleke ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi, tun daga wakiltar mazabar Osun ta Yamma a matsayin Sanata, har zuwa zama Gwamnan Jihar Osun a ƙarƙashin PDP.
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa a 'yan kwanakin nan, an yi ta ce-ce-ku-ce kan inda Gwamna Adeleke zai dosa sakamakon rigimar da ke kara kamari a PDP.
Gwamna Adeleke, wanda zai gama wa'adinsa na farko nan kusa, ya fara shiga matsala ne sakamakon shirinsa na neman tazarce amma ya rasa bangaren da zai kama a PDP.

Source: Twitter
Wace jam'iyyar gwamnan Osun zai koma?
Har ila yau, rahotanni marasa tabbaci sun yi nuni da yiwuwar Gwamna Adeleke ya koma jam'iyyar Accord Party, yayin da zaɓen gwamnan jihar Osun na 2026 ke ƙaratowa.
A shekarar 2026, hukumar zabe mai zaman kanta a watau INEC ta shirya gudanar zaben gwamnana a jihar Osun.
An shawarci Gwamna Adeleke ya shiga AP
A wani rahoton, kun ji cewa wani jigon PDP, Prince Olagunsoye Oyinlola, ya bukaci Gwamna Adeleke ya fara neman jam'iyyar da ya kamata ya koma don kaucewa abin da ka iya faruwa a PDP .
Oyinlola, ya ce jam'iyyar AP ce ta fi dacewa da Gwamna Adeleke don samun tikitin takarar neman tazarce a zaben Osun mai zuwa a shekarar 2026.
Ya kara da cewa ayyukan alherin da Adeleke yake yi ya wadatar wajen shawo kan kowa ya bi shi zuwa jam’iyyar da ya zaba domin mutanen sun ba su shirya gwada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

