Amaechi Ya Fadi Matsayarsa bayan an Fara Batun Ya Zama Mataimakin Atiku a 2027
- Na kusa da Atiku Abubakar, Dele Momodu, ya bayyana cewa tsohon dan takarar shugaban kasar na iya zabar Rotimi Amaechi a matsayin abokin takara
- Rotimi Amaechi ya fito ya nuna cewa bai da shirin zaman mataimaki ga kowane dan takara a zaben 2027 da za a tunkara
- Tsohon ministan sufurin ya sake jaddada aniyarsa ta gwada sa'arsa wajen neman takarar shugaban kasa yadda ya yi a 2023
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan batun zama mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2027.
Amaechi ya musanta zancen da ake yadawa cewa zai iya zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa ga Atiku, ko shiga wani tikitin haɗaka don zaben shugaban kasa a 2027.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa Amaechi ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, David Iyofor.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara batun takarar Atiku-Amaechi
Wannan bayanin ya biyo bayan kalaman na kusa da Atiku kuma ɗan jarida, Dele Momodu, ya yi, inda ya nuna yiwuwar Amaechi ya zama mataimakin Atiku idan Peter Obi ya ki amincewa da tikitin haɗin gwiwa a jam’iyyar ADC.
Dele Momodu ya ce Atiku na iya zabar Amaechi idan Peter Obi ya ki amincewa ya zama mataimakinsa.
“Mutane da yawa suna raina Amaechi. Shi ne ya taka babbar rawa wajen kai Buhari mulki. Abin da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke yi yanzu ko da yake ba a cikin tsari ba Amaechi ya yi shi yadda ya kamata a lokacin da yake gwamnan Rivers.”
“Amaechi ya fi kowa taimaka wa Buhari, har ma fiye da Tinubu. Idan Obi bai yanke shawara ba ko ya zaɓi yin takara shi kaɗai, ina ganin tikitin zai koma hannun Amaechi.”
- Dele Momodu
Me Amaechi ya ce kan zama mataimakin Atiku?

Kara karanta wannan
Bayan komawa ADC, Atiku ya fara zawarcin mutanen da za su yi masa mataimaki a 2027
Sai dai, Amaechi ya bayyana cewa baya neman zama mataimaki ga kowa, domin burinsa shi ne neman shugabancin kasa kai tsaye.
“Amaechi ba ya neman zama mataimakin shugaban kasa ga kowa. Ba ya kuma sha’awar zama ɗan takarar mataimaki a karkashin kowa, kuma ba zai zama ba.”
- David Iyofor
Ya ce babu wata tattaunawa da aka yi da Amaechi wajen zama mataimaki, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar da hakan.
“Don sake jaddadawa, Amaechi yana neman zama shugaban Najeriya, ba mataimaki ga wani ba.”
- David Iyofor

Source: Facebook
David Iyofor ya gargadi ’yan siyasa da su daina saka sunan Amaechi cikin duk wata jita-jitar takarar mataimakin shugaban kasa.
A baya Amaechi ya sha bayyana cewa ya cika ka’idar zama Shugaban Najeriya, inda ya yi nuni da tarihin aikinsa da gogewarsa a siyasa.
Amaechi ya ba 'yan adawa shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi muhimmin kira ga 'yan adawa kan zaben 2027.
Rotimi Amaechi ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su tashi tsaye kafin babban zaben 2027 da ake tunkara.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya jaddada cewa za a iya kayar da Shugaba Bola Tinubu idan 'yan adawa suka hada kai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

