Natasha Ta Yi Barazana ga Sanata kan Sakon WhatsApp, Ta Sha Alwashin Tona Asiri
- An samu ce-ce-ku-ce a tsakanin al'umma bayan Sanata Natasha Akpoti ta rubuta wa Sanata Osita Ngwu gargaɗi kai tsaye a shafinta na sadarwa
- Natasha ta bukaci Ngwu ya bude dandalin WhatsApp na majalisar sannan ya dawo da sharhin da ya goge
- Martanin jama’a ya rarrabu, wasu na ganin tana neman rigima, yayin da wasu ke ganin jarumtar ta don bayyana gaskiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Sanata Natasha H. Akpoti daga jihar Kogi ta yi barazana ga wani sanata a Najeriya game da sakon WhatsApp.
Natasha ta ba shi sharadi da cewa idan har bai yi ba, za ta tona asirin abin da ke faruwa ga al'umma kowa ma ya sani.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani rubutu da Sanatar ta yi a shafinta na Facebook a yau Lahadi 30 ga watan Nuwambar 2025 da muke ciki.
Rigimar da ya jawo dakatar da Natasha
Natasha ta sha samun rigima da sauran sanatoci a majalisar tun bayan karambattar da tayi da shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
Daga bisani, bayan lamari ya faskara, an yanke shawarar dakatar da ita daga shiga majalisar har na tsawon watanni shida.
Lamarin ya jawo suka daga bangarori da dama a kasar inda wasu ke zargin ana neman kulle mata baki.
Duk da haka wasu na ganin sharri kawai take yi saboda ba shi ne karo farko ba da take irin haka ga manya a Najeriya.
Natasha ta dawo majalisa
Bayan dakatarwar watanni shida, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma bakin aiki a zaman Majalisar Dattawa.
Natasha ta isa zauren Majalisa da misalin karfe 11:52 jim kadan bayan shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karbi jagorancin zaman.
Rahotanni sun nuna cewa Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta gaisa da wasu sanatoci kafin ta zauna a kujerarta.

Source: Facebook
Gargadin Natasha ga Sanata kan sakon WhatsApp
Natasha ya bukaci Sanatan ya yi gaggawar dawo da sakon da aka goge domin gujewa matakin da za ta dauka kan haka.
A cikin rubutunta, Natasha ta ce:
"Ya kai Sanata Osita Ngwu da ke wakiltar mazabar Enugu ta Yamma a majalisa.
"Ka bude dandalin WhatsApp na majalisar dattawa sannan ka sake saka sakon na da ka goge, idan ba haka ba, zan bayyana bayanai ga al'umma su sani."
Wannan rubutu na Natasha ya jawo martani a tsakanin al'umma musamman masu ta'ammalai da kafofin sadarwa ta Facebook.
Wasu daga cikin masu sharhi sun gargadi Natasha da ta yi hankali da mutanen nan fa saboda za su kawo karshen siyasarta.
Yayin da wasu ke yi mata ba'a da cewa ta cika neman rigima, wasu ko kiranta suke yi jaruma saboda yadda ta ke nuna rashin tsoro.
Natasha ya soki jami'in NIS a filin jirgi
Mun ba ku labarin cewa an fafata tsakanin jami'an Hukumar NIS da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanata Natasha ta je filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ranar Talata 4 ga watan Nuwambar 2025 da nufin tafiya hutun mako guda a kasar waje.
Sanatar Kogi, Natasha ta bayyana cewa bayan shafe tsawon lokaci ana takaddama, hukumar NIS ta maida mata da fasfo dinta.
Asali: Legit.ng


