Zaben 2027: Atiku Ya Hango Jam'iyyar da Za Ta Ceto 'Yan Najeriya daga Hannun APC

Zaben 2027: Atiku Ya Hango Jam'iyyar da Za Ta Ceto 'Yan Najeriya daga Hannun APC

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi tsokaci kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Atiku Abubakar ya bayyana cewa APC ta jefa 'yan Najeriya cikin halin kakani-kayi a shekarun da ta kwashe tana mulki a kasar nan
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna ADC ce kadai zabin da 'yan Najeriya suke da shi domin ceto su daga halin da suka tsinci kansu a ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Taraba - Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan zaben 2027.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ce kadai mafita da za ta ceci ’yan Najeriya daga halin wahala da suka tsinci kansu a karkashin gwamnatin APC mai ci.

Atiku ya yi magana kan zaben 2027
Atiku Abubakar da tambarin jam'iyyar ADC Hoto: @atiku
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa Atiku ya bayyana hakan a birnin Jalingo yayin bude ofishin ADC na jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Atiku ya ce kan zaben 2027?

Atiku ya ce ADC na da cikakkiyar damar lashe zaben 2027, amma dole ne ’yan Najeriya su hada kai domin su kasance cikin wadanda za su kubutar da kasar daga halin da take ciki.

Ya yi kira ga dukkan mutanen da suka cancanta, musamman mazauna Taraba, da su yi rajistar katin zabe sannan su karɓi PVC dinsu.

Atiku ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na canja gwamnati a 2027 ba zai yiwu ba muddin jama’a ba su mallaki damar kada kuri’arsu ba.

Atiku ya kuma caccaki gwamnatin APC mai ci, yana mai cewa ba ta yi komai ba wajen inganta rayuwar ’yan Najeriya.

Ya kara da cewa shugabannin ADC kwararru ne, kuma za su yi aikin da ya fi na gwamnati mai ci muddin aka basu amanar jagoranci a matakin tarayya da jihohi a 2027.

Jam'iyyar ADC ta kafa kwamiti a Taraba

Kara karanta wannan

Atiku: "Ba a taba jam'iyyar da ta azabtar da 'yan Najeriya kamar APC ba"

A nasa bangaren, shugaban ADC na jihar Taraba, Hassan Adamu, ya ce jam’iyyar ta zama zabin jama’a a jihar, kuma za ta zama wata madaidaiciyar hanya ta kawo sauyi a zaben 2027.

Hakazalika an kuma kafa kwamitin mika mulki na jam’iyyar a jihar, inda Sanata Abubakar Tutare ya zama shugaban kwamitin, yayin da Barista Haruna Kwetishe ya zama sakatare.

Karanta wasu labaran kan Atiku Abubakar

Oshiomhole ya yi wa Atiku shagube

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Adams Oshiomhole, ya taso Atiku Abubakar a gaba kan sauya sheka zuwa ADC.

Sanata Adams Oshiomhole ya jaddada cewa Atiku ba zai iya gyara Najeriya ba idan har bai iya gyara tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ba.

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya ce Atiku ya dade yana fafutukar daidaita PDP amma hakan ya kasa tabbata, don haka ya rasa hujjar cewa zai iya daidaita al’amuran kasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng