Jonathan Ya ga Abin Mamaki a Guinea Bissau, Kasar da Ya Makale bayan Juyin Mulki

Jonathan Ya ga Abin Mamaki a Guinea Bissau, Kasar da Ya Makale bayan Juyin Mulki

  • Goodluck Jonathan ya bayyana cewa abin da ya faru a Guinea Bissau ya fi masa ciwo fiye da kaye da ya sha a zaben 2015
  • Ya ce ba a taba ganin irin wannan yanayi ba, inda shugaban ƙasa Umaro Embaló da kansa ya fara sanar da juyin mulki
  • Jonathan ya bukaci ECOWAS da AU su fitar da cikakken sakamakon zaben da aka yi a kasar tare da sakin Fernando Dias

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana alhini kan abin da aka kira juyin mulki a kasar Guinea Bissau.

Jonathan ya yi magana yana mai cewa lamarin ya fi masa zafi fiye da ranar da ya kira Muhammadu Buhari ya taya shi murna bayan shan kaye a zaben 2015.

Kara karanta wannan

Ngige: Ministan Buhari ya fadawa Obi yadda 'yan ta'adda suka bude masa wuta

Goodluck Ebele Jonathan
Lokacin da Jonathan ke duba zabe a Guinea Bissau. Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Jonathan da ya je Guinea Bissau a matsayinsa na memba a WAEF domin sa ido kan zaben shugaban ƙasa da na majalisa, ya ce wannan lamari ya girgiza shi matuƙa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin Jonathan kan Guinea Bissau

Bayan dawowa Najeriya daga Guinea Bissau, Goodluck Jonathan ya ce ya ce abin da aka kira juyin mulki a kasar ya ba shi mamaki matuka:

“Abin da ya faru a Guinea Bissau abin tayar da hankali ne gare ni, musamman ni da nake ɗaya daga cikin masu fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya.
Gaskiya, na ji zafi fiye da ranar da na kira Buhari na taya shi murna bayan na fadi zabe ina rike da mulki.”

Ya ce tun tashe-tashen hankulan 2012 da rikicin da ya biyo baya, ya kasance cikin waɗanda suka jajirce wajen tabbatar da gudanar da zaben 2013 a Guinea Bissau ba tare da tangarda ba.

“Ba juyin mulki ba ne, ” Shugaba Jonathan

Kara karanta wannan

'Tausayinsa na ke ji': Malami ya yi magana bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Jonathan ya ce abin da ya faru bai yi kama da juyin mulki ba saboda yadda shugaban ƙasar Embaló ya fara sanar da cewa an yi juyin mulki.

Ya ce abin mamaki ne shugaban kasa yana sanar da juyin mulki yayin da yake amfani da wayarsa yana magana da kafafen watsa labarai na duniya.

Ya ce rahotannin AU da ECOWAS sun tabbatar da cewa zaben ya gudana lafiya, amma kafin a kammala kirga sakamakon, sai Embaló ya ce an kama shi.

A cewarsa:

“Abin ya bani mamaki cewa shi shugaban ƙasa ne ya fara sanar da cewa an yi juyin mulki, sannan daga baya sojoji suka fito.
"Haka ba ta faruwa a ko’ina. Idan aka yi juyin mulki, shugaban ƙasa ba ya yawo da waya yana hira da duniya.”
Sojoji kasar Guinea Bissau
Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea Bissau. Hoto: Getty Images
Source: AFP

Jonathan ya cigaba da cewa irin wannan salon ba ya faruwa a juyin mulki na gaskiya, musamman a lokacin da ake gab da bayyana sakamakon zabe.

Rahoton Channels TV ya nuna cewa Jonathan ya bukaci sakin shugaban adawa Fernando Dias, yana mai cewa ba shi da wani laifi da zai sa a tsare shi.

Kara karanta wannan

Majalisa ta tsoma baki da Jonathan ya makale a kasar da sojoji suka yi juyin mulki

Yadda Jonathan ya makale a Guinea Bissau

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya makale a Guinea Bissau bayan juyin mulki.

A lokacin da ya makale, wasu daga cikin jami'ansa sun bayyana cewa yana cikin koshin lafiya duk da bai samu damar fita daga kasar ba.

'Yan majalisar tarayya sun yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kubutar da shi kafin daga baya ya baro kasar zuwa Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng