‘Zan Yi Murabus idan Tinubu Bai Ci Jiha Ta ba’: Gwamna game da Zaben 2027

‘Zan Yi Murabus idan Tinubu Bai Ci Jiha Ta ba’: Gwamna game da Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi wa Bola Ahmedd Tinubu alkawari mai girma game da zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Okpebholo ya ce babu wani dan adawa da ya rage a Edo yana tabbatar da cewa mutanen jihar gaba ɗaya suna goyon bayan Bola Tinubu
  • Gwamnan ya ce ayyukan da gwamnatin APC ta aiwatar sun sa Tinubu ya fi shahara a Edo, yana jaddada cewa jama’a sun gama yanke shawarar zabe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Edo - Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana irin farin jini da Bola Ahmed Tinubu ke da shi a tsakanin al'ummar jihar.

Okpebholo ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 a jihar Edo ba tare da shakka ba.

Gwamna ya yi alkawarin miliyoyin kuri'u ga Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Monday Okpebholo. Hoto: Bayo Onanuga, Sen. Monday Okpebholo.
Source: Facebook

Gwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafofin sadarwa wanda Pro Samson Oluwadamilola ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamna Nasir ya ba daliban da 'yan bindiga suka saki a Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya roki Musulmai alfarma kan Tinubu

Ko a kwanakin baya ma, Gwamna Okpebholo ya roki al'ummar Edo musamman Musulmi da su zabi Bola Tinubu idan zaben 2027 ya karato.

Gwamna Okpebholo ya yi kira ga al’ummar Musulmi su ci gaba da marawa Shugaba Bola Tinubu baya domin ci gaba da kawo ayyukan alheri.

Okpebholo ya ce goyon bayansu na da matuƙar muhimmanci ga nasarar sauye-sauyen da gwamnati ke yi.

Gwamna ya sha alwashin yin murabus idan Tinubu bai ci zabe a Edo ba
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo. Hoto: Sen. Monday Okpebholo.
Source: Twitter

Yawan kuri'u da gwamna ya yi alkawari ga Tinubu

Gwamnan ya sake nanata alkawarin kawo Tinubu kan gaba a zaben 2027, ciki har da niyyarsa ta samar da kuri’u miliyan 2.5 daga Edo.

Gwamnan ya kara da cewa zai yi murabus idan har Bola Tinubu ya gaza lashe zaben jihar Edo saboda irin ayyukan alheri da ya yi musu.

Okpebholo ya ce al’ummar Edo sun gama yanke shawara kan wanda za su zaba, yana danganta goyon bayan da Tinubu ke samu da ayyukan da gwamnatin APC ta aiwatar tun bayan karɓar mulki.

Kara karanta wannan

'Maganganun Tinubu ne suka jawo': Ministan Buhari kan karuwar rashin tsaro

Ya kara da cewa babu wata jam’iyyar adawa a jihar, domin kowa yana tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan shugaban kasar.

A cewarsa, Tinubu ya fi shi shahara a cikin jihar saboda yadda jama’a suka amince da manufofinsa inda ya ce sun shirya saka masa da alheri.

A cewarsa:

“Babu wata jam’iyyar adawa a nan Edo, kowa yana goyon bayan Asiwaju a wannan jiha.
“Tinubu ya fi ni shahara a jihar Edo. Idan bai yi nasarar zaben shugaban kasa a Edo a 2027 ba, zan yi murabus.”

Musulmai sun shiga kotu da gwamnan Edo

A baya, mun sanar muku cewa Gwamna Monday Okpebholo zai kare kansa bayan kungiyar Musulmi ta maka shi da gwamnatinsa game da makarantar gwamnati.

Musulmai a jihar Edo sun kai gwamnati kotu kan mika makarantun gwamnati ga cocin Katolika ba tare da tuntubar sauran bangarori ba.

Masu kara sun ce matakin ya sabawa sashe 38 da 42 na kundin tsarin mulki, suna neman kotu ta hana sake mika makarantun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.