El Rufai Ya Bi Sahun Atiku wajen Shiga ADC, Ya Sha Alwashi kan APC a Zaben 2027
- Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta samu sabon mamba a jihar Kaduna da Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya shiga cikinta
- Tsohon gwamnan na Kaduna ya shiga ADC ne a hukumance a ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 bayan ya karbi katin zama mamba
- Nasir El-Rufai ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ta amince da sharudda da tsare-tsaren da 'yan hadaka suka gabatar mata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shiga jam’iyyar ADC a hukumance.
Nasir El-Rufai ya shiga ADC ne watanni bayan barin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta tattaro cewa tsohon gwamnan ya yi rajista da ADC tare da karɓar katin zama mamba a ofishin jam’iyyar da ke mazabarsa ta Unguwar Sarki, Kaduna.
Nasir El-Rufai ya shiga jam'iyyar ADC
Tsohon ministan na babban birnin tarayya Abuja ya samu rakiyar magoya bayansa, ciki har da tsofaffin masu rike da mukamai da shugabannin kananan hukumomi, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.
El-Rufai ya yi alkawarin amfani da jam’iyyar ADC wajen kalubalantar abin da ya kira rashin iya mulki a jihar.
“Ni cikakken mamba ne na jam’iyyar ADC. SDP ta ki bude kofa ga 'yan hadaka saboda gwamnati ta ba wasu shugabanninta cin hanci."
"Abin farin ciki, ADC ta amince da sharudda da tsarin jagorancin wannan hadaka.”
- Nasir El-Rufai
Ya ce an kammala dukkan zabubbukan cike gurbi da wasu kararraki na siyasa da suka jinkirta shigarsa cikin jam’iyyar.
El-Rufai zai kalubalanci APC a Kaduna
A wajen magana kan siyasa, El-Rufai ya yi alkawarin kalubalantar shugabancin APC a Kaduna.
“Ina kira ga duk ’yan jihar Kaduna masu shekaru 18 da sama su fito kwansu da kwarkwarsu su yi rajista da jam’iyyar ADC."
"Da ikon Allah, za mu maimaita abin da muka yi a 2015, lokacin da muka kawar da gwamnatin PDP mai rashin iya aiki, satar dukiya, da cin amanar jama’a.”
- Nasir El-Rufai

Source: Facebook
Malam El-Rufai ya soki gwamnatin APC
Haka kuma ya zargi gwamnatin APC ta yanzu a jihar da gazawa wajen cika alkawura, tare da yin mulki na rashin bin doka da oda.
“Mu muka taimaka wajen kawo su mulki. Don haka muna da hakkin taimakawa wajen dawo da su gida kafin ma su tafi gidan yari.”
- Nasir El-Rufai
Rajistar ta kasance mai cike da muhimmanci, domin El-Rufai ya karɓi lambar mamba na 000002, bayan mataimakin shugaban hadaka a Arewa maso Yamma wanda ya samu 000001 a matsayin mamba na farko a jihar.
Atiku ya shiga jam'iyyar ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC a hukumance.
Atiku Abubakar wanda ya kasance jagoran 'yan hadaka ya koma ADC ne bayan ya dade da ficewa daga jam'iyyar PDP.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yanki katin zama mamba a jam'iyyar ADC a mazabarsa da ke Jada a jihar Adamawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

