Jonathan Ya Makale a Guinea Bissau, Sojoji Sun Rufe Kasar bayan Juyin Mulki

Jonathan Ya Makale a Guinea Bissau, Sojoji Sun Rufe Kasar bayan Juyin Mulki

  • Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya makale a Guinea Bissau bayan sojoji sun sanar da juyin mulki tare da rufe iyakokin ƙasar
  • Sojojin sun dakatar da tsarin zaɓe, yayin da daruruwan masu sa ido daga ƙasashen waje suka makale a filin jirgin sama a yammacin jiya
  • An tabbatar da cewa Jonathan na cikin aminci, amma yana cikin rukuni na jami’an sa ido da ba za su iya barin ƙasar ba saboda wasu dalilai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Guinea Bissau – Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya makale a Guinea Bissau bayan rundunar sojan ƙasar ta sanar da juyin mulki.

Jonathan yana ƙasar ne a matsayin jagoran tawagar sa ido ta WAEF da ta tafi duba zaɓukan da aka gudanar a ranar 23, Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da Oke, Are da Dalhatu, sababbin jakadu da Tinubu ya nada

Jonathan yayin duba zabe a kasar Guinea Bissau
Lokacin da Jonathan ya fito aiki a kasar Guinea Bissau. Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa bayan sanarwar kifar da gwamnati, daruruwan masu sa ido daga ƙasashen waje sun yi ƙoƙarin barin ƙasar, amma rufe dukkan iyakoki ya sa suka makale.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin da suka aiwatar da juyin mulkin sun bayyana cewa sun samu “cikakken iko” bayan manyan ‘yan takara biyu sun yi iƙirarin nasara.

Sojojin sun karɓi mulki a Guinea Bissau

A cewar rahotanni, gungun hafsoshin soja ya sanar da dakatar da duk wani abu da ya shafi zaɓe har zuwa wani lokaci da za a sanar.

Haka nan, sojojin sun bayar da umarnin rufe iyakokin ƙasa, teku da sama, tare da kafa dokar hana fita na dare.

Shugaban ƙasa Umaro Sissoco Embalo ya ce an kifar da gwamnatinsa, inda ya shaida cewa:

“An tumɓuke ni daga mulki, kuma ina a hedikwatar rundunar sojoji a yanzu.”

Haka nan, shugaban jam’iyyar adawa ta PAIGC, Domingos Simoes Pereira, ya shiga hannu, inda rahotanni suka nuna cewa ana ƙoƙarin katse intanet a fadin ƙasar kuma an sanya dokar hana fita.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje, 'yan APC sun fitar da 'dan takarar shugaban kasa da suke so a 2027

Hassan Haque ya ce jami’in soja da ke jagorantar juyin mulkin, Denis N’Canha, shi ne ya taɓa zama shugaban tsaron fadar shugaban ƙasa.

Halin da Jonathan ke ciki a Guinea Bissau

Kokarin tabbatar da inda Jonathan yake da lafiyarsa daga mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, bai yi nasara ba domin layin wayarsa baya tafiya.

Sai dai tsohon mai magana da yawun Jonathan, Ima Niboro, ya tabbatar da cewa yana Guinea Bissau lokacin da lamarin ya faru, kuma yana cikin aminci duk da cewa ya makale.

The Cable ta rahoto cewa Niboro ya shaida cewa ya samu magana da mutanen da ke tare da Jonathan, kuma sun tabbatar masa cewa:

“Yana lafiya, amma ya makale tare da sauran jami’an sa ido.”
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan yana wani jawabi. Hoto: Goodluck Ebele Jonathan
Source: Facebook

Shekara 68: Tinubu ya taya Jonathan murna

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya Goodluck Jonathan murnar cika shekara 68.

Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce Bola Tinubu yana yi wa Jonathan fatan alheri tare da rokon Allah ya masa tsawon rai.

Kara karanta wannan

Ba a gama da jihohin Kebbi da Neja ba, an sace mata a jihar Borno

Haka zalika shugaban kasar ya yaba da rawar da Jonathan ya taka wajen kare dimokuradiyyar Najeriya a shekarun baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng