Osun 2026: Bayan APC Ta Rufe Kofa, An Bukaci Gwamna Ya Sauya Sheka zuwa AP

Osun 2026: Bayan APC Ta Rufe Kofa, An Bukaci Gwamna Ya Sauya Sheka zuwa AP

  • Alamu na nuna Gwamna Ademola Adeleke na Osun ya fara laluben jam'iyyar da zai nemi tazarce a karkashin inuwarta a zaben 2026
  • Tsohon gwamnan Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola ya ce ya fara tattaunawa da Gwamna Adeleke domin neman mafita
  • Ya ce a shawararsa, jam'iyyar Accord watau AP ce ta dace Gwamna Adeleke ya nemi tazarcen a zaben gwamna da za a yi a badi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Yayin da ake ganin babu tabbacin PDP za ta ba Gwamna Ademola Adeleke tikitin neman tazarce a zaben gwamnan Osun 2026, an fara lalubo masa mafita.

Wani jigon PDP, Prince Olagunsoye Oyinlola, ya bukaci Gwamna Adeleke ya fara neman jam'iyyar da ya kamata ya koma don kaucewa abin da ka iya faruwa a PDP.

Kara karanta wannan

Oshiomowhole: Tsohon shugaban APC ya yi wa Atiku shagube kan komawa ADC

Gwamna Ademola Adeleke.
Hoton gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke a cikin magoya baya Hoto: @AAdeleke1
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Oyinlola ya tantance jam'iyyu irinsu APGA, NNPP da sauran jam'iyyu tare da ba Gwamna Adeleke mafitar inda ya kamata ya dosa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace jam'iyyar ake so Adeleke ya shiga?

Olagunsoye Oyinlola, ya ce jam'iyyar AP ce ta fi dacewa da Gwamna Adeleke don samun tikitin takarar neman tazarce a zaben Osun mai zuwa a shekarar 2026.

Ya ce jam'iyyar hadakar 'yan adawa watau ADC ba ta kai matakin da ya kamata a nemi kujerar gwamna ba don har yanzu ba ta zauna da kafarta ba.

A wata hira da aka shi, tsohon gwamnan na Osun ya ce zai kammala tattaunawa da Adeleke kan shirin sauya shekarsa idan ya dawo Najeriya.

An nemi gwamnan Osun ya kaucewa NNPP

Ya yi watsi da yiwuwar Adeleke ya yi la’akari da komawa APGA ko NNPP, yana mai cewa:

“Wasu na ganin APGA jam’iyyar Igbo ce, yayin da NNPP kuma jam’iyyar Hausawa ce. Abin da ke faruwa a jam’iyyarmu ta PDP wani abu ne da ke damun kowa, amma duk da haka, Gwamna Adeleke zai sami mafita.”

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya koma ADC

"Gwamnanmu yana son tazarce, sai dai kuma, rikicin da ke faruwa a matakin kasa na PDP, ba mu san inda zai kai ba. Bisa ga ka’idar INEC, dole jam’iyyu su kammala zaben fidda gwani kafin 15 ga Disamba, kuma rikicin PDP har yanzu bai lafa ba."
"Abin da za mu yi shi ne, da zarar gwamnan ya dawo, za mu kammala batun domin tuni muka fara tattaunawa."
Prince Olagunsoye Oyinlola.
Hoton jigon PDP a Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola Hoto: Olagunsoye Oyinlola
Source: Facebook

Ya kara da cewa ayyukan alhrin da Adeleke yake yi ya wadatar wajen shawo kan kowa ya bi shi zuwa jam’iyyar da ya zaba domin utanen Osun ba su shirya gwada wani sabo ba, cewar Vanguard.

Gwamnan Osun zai koma jam'iyyar ADC?

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Osun ta sake fitowa fili ta yi magana kan jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamna Ademola Adeleke zai bar PDP ya koma ADC.

Ta tabbatar da cewa babu wata tattaunawa tsakanin Gwamna Ademola Adeleke da tsohon gwamna Rauf Aregbesola kamar yadda ake yadawa.

Wannan ba shi ne karon farko da Gwamna Ademola Adeleke ya ke fitar da sanarwa inda yake kore rade-radn da ake yadawa kan cewa zai bar jam'iyyyar PDP ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262