Oshiomhole: Tsohon Shugaban APC Ya Yi Wa Atiku Shagube kan Komawa ADC

Oshiomhole: Tsohon Shugaban APC Ya Yi Wa Atiku Shagube kan Komawa ADC

  • Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Adams Oshiomhole, ya soki Alhaji Atiku Abubakar kan komawa jam'iyyar ADC
  • Adams Oshiomhole ya bayyana cewa Atiku ya gaza gyara tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP wadda ya zama mataimakin shugaban kasa a karkashinta
  • Sanatan ya tuna cewa Atiku na da tarihin sauya sheka, inda a baya ya fice daga APC bayan ya kasa samun tikitin takara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata Adams Oshiomhole ya ce Atiku Abubakar bai da kwarewar da ake bukata domin mulkar Najeriya.

Sanata Adams Oshiomhole ya jaddada cewa Atiku ba zai iya gyara Najeriya ba idan har bai iya gyara jam’iyyar PDP ba.

Oshiomhole ya yi wa Atiku shagube
Sanata Adams Oahiomhole da Alhaji Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Tsohon shugaban na APC ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya koma ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC

Maganganun Oshiomhole sun biyo bayan ficewar Atiku daga PDP da shiga ADC, jam’iyyar da wasu manyan ‘yan adawa suka dunkule a cikinta domin kalubalantar APC a zaben 2027.

Atiku ya tabbatar da sauya shekar tasa ne dai zuwa jam'iyyar ADC a ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamban 2025.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yanki katin zama cikakken dan ADC a mazabar Jada da ke jihar Adamawa.

Me Sanata Oshiomhole ya ce kan Atiku?

Oshiomhole ya ce Atiku ya dade yana fafutukar daidaita PDP amma hakan ya kasa tabbata, don haka ya rasa hujjar cewa zai iya daidaita al’amuran kasar nan.

“Idan Atiku a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa a karkashin PDP bai iya gyara jam'iyyar ba, bai iya gina ta ko samar da shugabanci ba, ta yaya zai ce zai gyara Najeriya?”

- Sanata Adams Oshiomhole

Ya kuma tuna cewa Atiku ya taba shiga APC amma ya bar jam’iyyar ne kawai saboda rashin samun takarar shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Jira ya kare: Atiku ya sa lokacin zama dan jam'iyyar ADC bayan ya dade da barin PDP

“Ya taba zama a APC. Ya fita ne saboda bai samu tikitin takara ba. Ya koma PDP saboda yana son takara."
“Ya koma PDP. Yana matukar son PDP akalla don yin takara a karkashinta. Ya kasa gina jam'iyyar PDP."
"To idan Atiku ba zai iya gina PDP da ta sanya ya zama mataimakin shugaban kasa ba, ba zai iya gyara Najeriya ba."

- Adams Oshiomhole

Oshiomhole ya yi wa Atiku shagube kan shiga ADC
Sanata Adams Oshiomhole a zauren majalisar dattawa Hoto: @TheoAbuAgada
Source: Twitter

Sauya shekar Atiku zuwa ADC na zuwa ne bayan rikice-rikicen da suka dabaibaye PDP, lamarin da ya sa ya yi murabus daga jam’iyyar a watan Yuli.

Oshiomhole ya ba Jonathan shawara kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya bada shawara ga Goodluck Jonathan kan fitowa takara a zaben 2027.

Adams Oshiomhole ya shawarci tsohon shugaban kasar na Najeriya, da kada ya amince da matsin lambar da wasu ke yi masa don shiga takarar shugabancin kasa a zaben 2027 da ake tunkara.

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya bayyana cewa yin takarar Jonathan a zaben shekarar 2027, na iya lalata martabarsa da kimarsa a siyasance.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng